Bidiyon Abba Kabir Ya Jagoranci Okpebholo zuwa ga Iyalan Wadanda Suka Mutu a Edo
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya karbi bakuncin Gwamna na Edo, Sanata Monday Okpebholo, domin tattaunawa kan kisan da aka yi wa Hausawa
- Taron ya mayar da hankali kan hanyoyin samar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin Kano da Edo bayan rikicin da ya yi sanadin rasa rayuka
- Gwamna Abba ya bukaci a gaggauta yin adalci ga wadanda abin ya shafa, tare da tabbatar da tsaro domin hana aukuwar irin haka nan gaba
- Gwamna Okpebholo ya bayyana jajensa ga al’ummar Hausawa, yana mai cewa gwamnatinsa za ta dauki matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya karbi bakuncin takwaransa na Edo, Sanata Monday Okpebholo bayan kisan Hausawa.
Gwamnan ya raka Okpebholo zuwa karamar hukumar Bunkure domin jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Asali: Twitter
Kisan Edo: Abba Kabir zai biya diyya
Hadimin Abba Kabir a bangaren yada labarai ta zamani, Abdullahi Ibrahim shi ya tabbatar da haka a yau Litinin 31 ga watan Maris, 2025 a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alkawura ga iyalan wadanda aka hallaka a garin Uromi da ke jihar Edo.
Abba Kabir ya nuna alhini kan kisan da aka yi wa ‘yan asalin Kano a Edo, yana mai cewa za su tabbatar an gurfanar da masu laifin da dakile faruwar haka a nan gaba.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar an biyan diyyar mutanen tare da kwato duk wani hakki na su ko na iyalansu.

Asali: Facebook
Gwamna Okpebholo ya gana da Abba Kabir
Kafin zuwa karamar hukumar Bunkure, Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya iso Kano domin jajanta wa Gwamna Abba Kabir da iyalan mutane 16 da aka kashe a Uromi, Jihar Edo
Okpebholo ya kai wannan ziyara ta musamman ne domin nuna alhinin abin da ya faru da mutanen da aka kashe a makon da ya gabata.
Sanarwar ta bayyana cewa Gwamnan Edo ya gana da Abba Kabir a gidan gwamnati domin jajanta masa da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Abba Kabir ya raka Okpebholo zuwa Bunkure
Hadimin Abba Kabir ya wallafa faifan bidiyo inda gwamnan ke raka takwaransa domin jajanta musu da kansa kan abin takaici da ya faru.
Sanarwar ta ce:
"Gwamna Abba Kabir Yusuf ya raka Sanara Monday Okpebholo zuwa karamar hukumar Bunkure domin yin jaje ga iyalan wadanda aka halaka a garin Uromi da ke jihar Edo a makon da ya gabata."
Gwamna Okpebholo ya gana da Barau Jibrin
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jIhar Edo, Monday Okpebholo ya kai ziyarar ta'aziyya ga Sanata Barau Jibrin kan kisan da aka yi wa ƴan Arewa a jiharsa.
Monday Okpebholo wanda ya nuna takaicinsa kan lamarin ya bayyana cewa ya zuwa yanzu an cafke wasu da ake zargin akwai hannunsu a lamarin.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tallafawa iyalan mamatan da suka rasa ransu a mummunan lamarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng