Bayan Kisan Hausawa, Gwamna Okpebholo Ya Dura a Kano, Ya Gana da Abba Kabir
- Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya isa Kano domin jajanta wa Gwamna Abba Kabir da iyalan mutane 16 da aka kashe a Uromi, Jihar Edo
- Okpebholo ya kai wannan ziyara ta musamman ne domin nuna alhinin abin da ya faru da mutanen da aka kashe a makon da ya gabata
- Hidimin Gwamna Abba Kabir, Abdullahi I Ibrahim, ne ya wallafa sanarwar zuwan Okpebholo a shafinsa na X a yau Litinin
- Sanarwar ta bayyana cewa Gwamnan Edo ya gana da Abba Kabir a gidan gwamnati domin jajanta masa da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Yayin da ake jimamin kisan ƴan Arewa 16, Gwamnan Edo ya shigo jihar Kano inda ya gana da Gwamna Abba Kabir.
Gwamna Monday Okpebholo ya kawo ziyara ta musamman ga Abba Kabir Yusuf domin jajanta masa kan abin bakin ciki da ya faru.

Asali: Twitter
Edo: Abba Kabir ya yi alhinin kisan Hausawa
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hidimin Abba Kabir, Abdullahi I Ibrahim ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ziyara na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya nuna damuwa kan kisan Hausawa da aka yi waɗanda mafi yawansu yan Kano ne.
Abba Kabir ya nuna alhini kan kisan da aka yi wa ‘yan asalin Kano a Edo, yana mai cewa za su tabbatar an gurfanar da masu laifin.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar an biya diyyar mutanen tare da kwato duk wani hakki na su ko na iyalansu.
Edo: Matakin da Abba Kabir ya dauka
Abba Kabir Yusuf ya ce ya hada tawaga ta musamman da za ta tashi daga Kano har zuwa Edo domin tattaunawa da Hausawan jihar da kuma gwamnan jihar kan lamarin.
Haka zalika ya bayyana cewa gwamnan Edo ya kira shi a waya kan lamarin, kuma ya tabbatar masa da cewa ana daukar matakin kama masu laifin.
Gwamnan ya ce an kama mutane da dama kuma za a tafi da su Abuja domin bincike da daukar matakin da ya dace.

Asali: Facebook
Gwamnan Edo ya gana da Abba Kabir
A cikin sanarwar, Ibrahim ya ce Gwamna Okpebholo ya iso gidan gwamnatin jihar Kano domin jajantawa iyalai da kuma Abba Kabir.
Sanarwar ta ce:
"Gwamnan Jihar Edo ya isa Fadar Gwamnatin Jihar Kano domin jajantawa gwamnati da iyalan mutane 16 da aka kashe a makon da ya gabata a Uromi, Jihar Edo."
Abba Hikima ya fasa zuwa Edo
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamiti don bin kadun kisan da aka yi wa ‘yan Arewa a Edo a makon jiya.
Lauya Abba Hikima da sauran lauyoyi sun dakatar da shirin zuwa Edo inda suka ce za su ba kwamitin dama domin yin aiki.
Sun bukaci a fitar da cikakken rahoto, a kamo wadanda suka aikata laifin, a kafa kotu ta musamman da kuma biyan diyya.
Sun nemi samar da tsaro a kudancin kasar, dokoki masu tsauri, da kafa kwamitin Arewa don tabbatar da ba a shashantar da lamarin ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng