Abba Hikima Ya Sauya Shawarar Zuwa Edo bayan Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamiti

Abba Hikima Ya Sauya Shawarar Zuwa Edo bayan Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamiti

  • Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti don bin kadun kisan da aka yi wa ‘yan Arewa a Edo a makon jiya
  • Lauya Abba Hikima da sauran lauyoyi sun dakatar da shirin zuwa Edo inda suka ce za su ba kwamitin dama domin yin aiki
  • Sun bukaci a fitar da cikakken rahoto, a kamo wadanda suka aikata laifin, a kafa kotu ta musamman da kuma biyan diyya
  • Sun nemi samar da tsaro a kudancin kasar, dokoki masu tsauri, da kafa kwamitin Arewa don tabbatar da ba a shashantar da lamarin ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti don bin kadun wadanda aka kashe 'yan Arewa a jihar Edo.

Bayan gwamnatin jihar ta kafa kwamiti domin bincike da tabbatar da hakkokin mutanen, lauya Abba Hikima da abokansa sun dakatar da zuwa jihar domin bin kadu.

Kara karanta wannan

Atiku ya mayar da hankali kan tausaya wa talaka a sakon barka da sallah

Abba Hikima sun sauya shawarar zuwa Edo kan kisan Hausawa
Abba Hikima ya fasa zuwa Edo bayan gwamnatin Kano ta kafa kwamiti. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Abba Hikima.
Asali: Facebook

Edo: Matakin da Abba Hikima suka ɗauka

Lauya Abba Hikima shi ya tabbatar da haka a yau Litinin 31 ga watan Maris, 2025 a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan da Abba Hikima da Alhaji Hamza Nuhu Dantani sun sanar da janye shirin tafiyarsu zuwa Edo domin tattara bayanai da fara neman hakkin mutanen nasu.

A cewarsu, sun yanke wannan shawara ne saboda suna da tabbacin cewa kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa zai yi aikin da ya dace.

Abba Kabir ya kafa kwamiti kan kisan Hausawa a Edo
Lauya Abba Hikima ya fasa zuwa Edo bayan gwamnatin Kano ta kafa kwamiti na musamman. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Bukatun Abba Hikima ga kwamitin da aka kafa

A cikin bayanan da aka fitar, Abba Hikima bayyana wasu bukatu da suka wajaba a yi don tabbatar da adalci.

Daga ciki akwai gaggauta bincike da fitar da cikakken rahoto kan yawan wadanda aka kashe, aka jikkata ko aka yi wa asarar dukiya.

Sai kamo duk masu hannu a lamarin, musamman jami’an vigilante da ake zargi da hannu a kashe-kashen.

Kara karanta wannan

Gwamnan Sokoto ya yi magana da babbar murya kan kisan 'yan Arewa a Edo

Sannan samar da kotun musamman domin tuhumar wadanda ake zargi da aikata wannan kisan gilla da hukuntasu cikin gaggawa.

Daga ciki akwai biyan diyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu tare da basu hakuri a hukumance.

Sai samar da jami’an tsaro a yankunan kudancin Najeriya don kare matafiya da direbobi daga irin wadannan hare-hare.

Akwai kuma tabbatar da doka ta musamman don hukunta masu daukar doka a hannu (mob action) don hana maimaituwar irin wannan ta’asa.

Sai na karshe, kafa kwamiti na musamman da zai kunshi wakilan Arewa domin sa ido kan lamarin da tabbatar da an dauki matakan da suka dace.

Jagororin sun bayyana cewa suna da kyakkyawan fata ga wannan kwamiti da aka kafa kuma suna fatan za a aiwatar da wadannan bukatu cikin gaggawa domin hana irin wannan faruwa nan gaba.

Edo: Abba Kabir ya magantu kan kisan Hausawa

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya nuna alhini kan kisan da aka yi wa ‘yan asalin Kano a Edo, yana mai cewa za su tabbatar an gurfanar da masu laifin.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar an biya diyyar mutanen tare da kwato duk wani hakki na su ko na iyalansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng