Tinubu Ya Fadi Barazanar da Ya Yi Wa Wike kan Rasa Mukaminsa, Ya ba Shi Mamaki
- Shugaba Bola Tinubu ya ce ya yi barazanar korar Minista Nyesom Wike idan manufofinsa ba su dace da bukatun jam’iyyar APC mai mulki ba
- Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da Wike shi ya jagoranci manya a Abuja don kai masa gaisuwar Sallah bayan kammala azumin Ramadan
- Shugaban kasa ya yaba wa Wike kan ayyukan inganta Abuja, ciki har da gyaran asibitoci, makarantu, da sabunta gidan mataimakin shugaban kasa
- Wike, wanda ke jam’iyyar PDP, ya ce aikinsa yana mayar da hankali ne kan ci gaban Abuja, duk da rade-radin siyasa da ke gudana
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana yadda ya yi wa Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, barazana.
Tinubu ya yi wa ministan barazanar kora idan manufofinsa ba su dace da bukatun jam’iyyar APC ba.

Kara karanta wannan
Hafsan tsaro ya tsoma baki kan kisan ƴan Arewa a Edo, ya fadi shirinsu kan lamarin

Asali: Facebook
Yadda Tinubu ya yi wa Wike barazana
Tinubu ya furta hakan ne a fadar shugaban kasa, Abuja, yayin da Wike ya jagoranci wasu fitattun mazauna Abuja don kai masa gaisuwar Sallah, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kasa ya tuna yadda Wike ya nemi cire Abuja daga asusun bai daya na TSA domin samun ‘yancin kudi da kuma inganta ayyukan raya birnin.
Ya kuma bayyana yadda ya jaddada muhimmancin la’akari da tasirin siyasa kafin yanke irin wannan shawara.
Tinubu ya ce:
"Ina tuna yadda Wike ya zo wurina ya ce, ‘Don Allah, cire mu daga wannan TSA domin in iya gudanar da aiki yadda ya kamata."
"Kuma ya gabatar da bukatarsa, ni kuma na ce, ‘Wannan zai taimaka wa jam’iyyata (APC) wajen samun nasara a zabe a Abuja?’”
"Na ce, ‘Na san inda kake, PDP ko APC? Idan wannan abu ya fi amfanar PDP, to za ka rasa aikinka.’ Sai ya ce, ‘Mun gama da maganar nan, Oga.’”

Kara karanta wannan
Sanatocin Arewa sun haɗa kai, sun taso da ƙarfi kan abin da aka yi wa ƴan Arewa a Edo

Asali: Facebook
Wike ya sha ruwan yabo daga Tinubu
Shugaba Tinubu ya yaba wa Wike bisa sauye-sauyen da ya kawo a birnin Abuja, musamman a fannin gine-gine, kiwon lafiya, da ilimi.
Ya kara da cewa:
“Ya zo da sababbin dabaru don kawar da matsaloli, ya habaka tunanin ci gaba, tare da samar da damammaki ga mutane."
Tinubu ya jero wasu daga cikin nasarorin Wike kamar gyaran gidan mataimakin shugaban kasa, gyaran asibitoci, da inganta yanayin makarantu.
Wike ya ce yana aiki ne don ci gaban Abuja, duk da ce-ce-ku-cen siyasa da ke gudana a tsakanin ‘yan adawa.
Shugaban kasa ya gode wa Wike, yana mai cewa, “Na gode, Wike,” domin yabawa da kokarin da ya yi a birnin tarayya.
Wike ya ja aya ga Atiku kan kalamansa
Mun ba ku labarin cewa Hadimin Wike, Lere Olayinka ya musanta ikirarin Atiku Abubakar cewa PDP ta fifita Okowa kan Wike a matsayin mataimakin takarar shugaban kasa na 2023.
Olayinka ya ce Atiku bai girmama azumin watan Ramadan ba saboda ya bayyana abin da ba gaskiya ba game da yadda PDP ta zaɓi ɗan takarar mataimakin shugaban kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng