Ana Zargin Matashi da Kisa a Tawagar Sanusi II, Ƴan Sanda Sun Gargadi al'ummar Kano

Ana Zargin Matashi da Kisa a Tawagar Sanusi II, Ƴan Sanda Sun Gargadi al'ummar Kano

  • Rundunar ‘yan sandan Kano ta cafke Usman Sagiru mai shekara 20 daga Sharifai kan zargin kashe wani dan sa-kai da harin da aka kai bayan sallar idi
  • A yayin watsewa daga filin sallah, Sagiru da wasu sun soka wa Surajo Rabiu wuka, wanda daga baya ya rasu, sannan Aminu Suleman na jinya a asibiti
  • An fara bincike kan lamarin, yayin da rundunar ‘yan sanda ta gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, don yi masa tambayoyi
  • Hukumar ta jaddada haramcin hawan sallah tare da gargadi kan aikata daba, tana mai cewa duk wanda ya saba doka zai fuskanci hukunc

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta cafke wani matashi mai suna Usman Sagiru kan zargin kisan kai.

An kama matashin mai shekara 20 daga unguwar Sharifai, bisa zargin hannu a kisan wani dan sa-kai da kai wa wasu hari tawagar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan

An farmaki ƴan Hisbah yayin hana ƙwallo a masallacin da ake tahajjud, sun samu raunuka

Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sarki Sanusi II
'Yan Sanda sun cafke wani da ake zargin ya kashe ɗan sa-kai a tawagar Sarki Sanusi II. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Asali: Facebook

Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sarki

Kakakin rundunar yan sanda a Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi 30 ga watan Maris, 2025 a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:40 na ranar yau Lahadi 30 ga watan Maris, 2024 a birnin Kano.

An bayyana cewa yayin da jama’a ke watsewa daga filin idi, Usman Sagiru da wasu da ba a kama ba sun soka wa wani dan sa-kai, Surajo Rabiu, wuka, wanda daga baya ya rasu.

Haka nan wani dan sa-kai, Aminu Suleman daga Kofar Mata, ya samu rauni kuma yana karbar magani a Asibitin Murtala Mohammed da ke Kano.

An cafke wani da zargin kisan kai a tawagar Sanusi II
Yan sanda sun kama matashi da ake zargin ya kashe dan sa-kai a tawagar Sanusi II. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi.
Asali: Twitter

Matakin da ƴan sanda suka ɗauka kan lamarin

Rundunar ta bayyana cewa ta fara gudanar da bincike kan lamarin tare da gayyatar Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, domin yi masa tambayoyi.

Kara karanta wannan

Hafsan tsaro ya tsoma baki kan kisan ƴan Arewa a Edo, ya fadi shirinsu kan lamarin

Hukumar ta ce tana daukar wannan lamari da matukar muhimmanci domin tabbatar da zaman lafiya a Kano.

Bugu da kari, ‘yan sandan sun jaddada cewa an haramta gudanar da duk wani biki na hawan sallah a Kano.

Haka nan an bayyana cewa duk wanda aka kama yana aikata daba ko wata harka da ka iya jefa tsaro cikin hadari, za a hukunta shi yadda doka ta tanada.

Rundunar ta bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu tare da yin hadin gwiwa da hukumomi domin tabbatar da zaman lafiya a Kano.

Edo: Sanusi II ya magantu kan kisan Hausawa

Mun ba ku labarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi Allah wadai da kisan 'yan Arewa da aka yi a jihar Edo, inda ya yi kira ga hukuma ta bi musu kadunsu.

Sarki Sanusi II ya nuna damuwa kan yadda aka yi wa mutanen Bunkure, Garko da Kibiya kisan gilla, yana mai cewa hakan rashin imani ne.

Basaraken ya bukaci al'umma su guji jita-jita da daukar doka a hannunsu, su saurari hukuncin da hukuma za ta yi domin zaman lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng