An Farmaki Ƴan Hisbah yayin Hana Ƙwallo a Masallacin da Ake Tahajjud, Sun Samu Raunuka

An Farmaki Ƴan Hisbah yayin Hana Ƙwallo a Masallacin da Ake Tahajjud, Sun Samu Raunuka

  • Rundunar ‘yan sandan Katsina ta cafke Alhaji Surajo Mai Asharalle da wasu uku kan zarginsu da kai wa jami’an Hisbah hari, inda suka jikkata su
  • Hisbah ta ce jami’anta sun je dakatar da matasa daga wasan ƙwallo kusa da masallaci, amma sai matasan suka bijire, suka kore su
  • A lokacin arangamar, Surajo Mai Asharalle ya harba bindiga sau da yawa, inda ya jikkata jami’an Hisbah biyar da ke bakin aiki
  • 'Yan sanda sun kama Surajo da abokan aikinsa uku, sun kwato bindigar, sannan aka kai waɗanda suka jikkata asibiti don samun kulawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama Alhaji Surajo Mai Asharalle da wasu mutum uku bisa zargin kai wa jami’an Hisba hari.

Rahotanni sun tabbatar da yayin harin, an jikkata jami'an hukumar Hisbah guda biyar a unguwar Kofar Kaura da ke birnin Katsina da ke Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku ya mayar da hankali kan tausaya wa talaka a sakon barka da sallah

An farmaki jami'an Hisbah a Katsina
Wasu matasa sun kai wa jami'an hukumar Hisbah hari a Katsina. Legit.
Asali: Original

Musabbabin abin da ya jawo hari kan Hisbah

Shafin Zagazola Makama shi ya tabbatar da haka a manhajar X a yau Lahadi 30 ga watan Maris din shekarar 2025 da muke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cewar wani jami'in hukumar Hisbah a Katsina, Nafi’u Aliyu Akilu, ya ce an kai harin ne da misalin ƙarfe 2:30 na asuba ana tsaka da sallar tahajjud a wani masallaci.

Ya ce hakan ya biyo bayan tura jami’ai domin dakatar da matasa da ke buga wasan ƙwallo kusa da masallacin da ake sallar Tahajjud cikin dare.

Amma lokacin da suka isa wurin, matasan sun bijire suka fatattaki jami’an hukumar na Hisbah wanda ya yi sanadin samun munanan raunuka daga ɓangarensu.

Wasu miyagu sun kai hari kan jami'an Hisbah a Katsina
Yan sanda sun cafke wani da zargin kai hari kan jami'an Hisbah a Katsina. Hoto: Hisbah Katsina Command.
Asali: Facebook

Yadda aka farmaki jami'an Hisbah a Katsina

A yayin arangamar, Surajo Mai Asharalle ya harba bindiga, ya jikkata jami’an hukumar Hisbah har guda biyar.

Daga cikinsu akwai Aminu Musa Yari, Muhammad Ibrahim, Yau Musa Ingawa, Kabir Abdullahi da Mustapha Isa.

Kara karanta wannan

An rasa rayuka 2, wasu 22 sun raunata a turmutsutsun filin idi, Gwamna ya yi bajinta

An tabbatar da cewa motoci har guda biyu kirar Peugeot 206 da Mercedes C180, sun lalace a wurin wanda ya jawo asara sosai ga masu su.

‘Yan sanda sun dira wurin, suka cafke Surajo da abokansa guda uku, sannan suka kai waɗanda suka jikkata asibiti.

Sai dai daga bisani, an kwashe su zuwa Asibitin Gwamnatin Tarayya domin kulawa da lafiyarsu.

Jami'in Hisbah ya yi magana da Legit Hausa

Wani jami'in hukumar Hisbah a Gombe ya ce abin takaici ne hari kan mutane da ke kokarin inganta tarbiyyar mutane.

Abbas Mohammed Dahiru ya ce Hisbah tana aiki matuka domin tabbatar da al'umma sun bi hanyar da ta dace.

Sai dai ya shawarci wasu daga jami'ansu su rika kula da wuraren da suke shiga saboda wasu ba su da tsari a rayuwa.

"A wannan yanki namu ne kawai za ka ga kana kokarin gyara amma wasu na yi maka zagon kasa saboda rashin sanin ciwon kai."

Kara karanta wannan

Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sanusi II, ƴan sanda sun gargadi al'ummar Kano

- Cewar Dahiru

Hisbah ta haramta gidajen casu a Katsina

Kun ji cewa Hukumar Hisbah a jihar Katsina ta haramta duk wani ayyukan gidajen gala da dare da kuma casu a fadin jihar baki daya domin tabbatar da daƙile tambadanci.

Wannan mataki ya biyo bayan kokarin kare dabi'u da kiyaye tsaron al'umma musamman da dare a fadin jihar yayin da ake shirin shiga watan azumi na Ramadan.

Kwamandan Hisbah, Aminu Usman, ya bukaci masu gidajen badala su rufe wuraren su, ya ce duk wanda ya saba doka zai fuskanci hukunci.

Hisbah ta bukaci hukumomin tsaro su tabbatar da bin wannan umarni kamar yadda ta haramta karuwanci da caca a fadin jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel