Sallah: Matawalle Ya Ware 'Yan APC, Ya Yi Musu Babbar Kyauta a Zamfara

Sallah: Matawalle Ya Ware 'Yan APC, Ya Yi Musu Babbar Kyauta a Zamfara

  • Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya tuna da ƴaƴan jam'iyyar APC a Zamfara yayin da aka kammala azumin watan Ramadan
  • Bello Matawalle ya yi wa mambobin APC sha tara ta arziƙi ta hanyar raba musi shanu domin su gudanar da bukukuwan Sallah cikin walwala
  • Ministan ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da sanya jami'an tsaron ƙasar nan a cikin addu'o'insu domin su samu nasara a yaƙin da suke da ƴan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Dr. Bello Matawalle, ya gwangwaje mambobin jam'iyyar APC da sha tara ta arziƙi a jihar Zamfara.

Bello Matawalle ya raba shanu sama da 100 ga mambobin APC a Zamfara domin tallafa musu wajen gudanar da bukukuwan ƙaramar Sallah cikin jin daɗi.

Matawalle ya raba shanu a Zamfara
Matawalle ya rabawa 'yan APC shanu a Zamfara Hoto: Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

Tashar Channels tv ta ce an gudanar da rabon shanun ne a birnin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

"Hantar Tinubu ta kaɗa": An faɗi wanda ya dace Atiku, Obi da El Rufai su marawa baya a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban APC na Zamfara Hon. Tukur Umar Danfulani, wanda sakataren jam’iyyar na jihar, Hon. Ibrahim Umar Dangaladima, ya wakilta, ya jagoranci taron.

Matawalle ya ba da tallafi a Zamfara

Da yake jawabi a wajen rabon shanun, Dr. Matawalle ya bayyana cewa wannan shiri yana daga cikin tsare-tsaren ba da tallafin watan Ramadan da yake gudanarwa kowace shekara.

Ya ce manufar rabon shi ne tallafawa mambobin jam’iyyar da kuma marasa galihu ta hanyar ba su abinci, nama, da tufafi domin su samu damar yin bukukuwan Sallah cikin farin ciki da annashuwa.

Ministan ya kuma jaddada cewa taimakon mabukata, musamman a lokacin azumin Ramadan, na ɗaya daga cikin koyarwar Manzon Allah (SAW), don haka ya buƙaci al’ummar musulmi su rungumi irin wannan ɗabi’a ta kyautatawa.

Bugu da ƙari, Dr. Matawalle ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ci gaba da yin addu’o’i ga jami’an tsaro na ƙasa, domin su samu nasara a yaƙi da ƴan ta’adda da sauran masu aikata laifuka.

Kara karanta wannan

Sallah: Sarkin Musulmi ya bukaci a fara duba watan Shawwal a Najeriya

Ya ce sojojin Najeriya na samun gagarumar nasara a ƙoƙarin murƙushe sansanonin ƴan bindiga a yankuna daban-daban na ƙasar nan.

Bello Matawalle
Matawalle ya raba shanu a Zamfara Hoto: Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

A cikin jawabinsa, ministan ya kuma tabbatar da cewa ma’aikatar tsaro za ta ci gaba da aiwatar da umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Arewa maso Yamma da ma ƙasa baki ɗaya.

Da yake magana a madadin APC a jihar, sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Mallam Yusuf Idris Gusau, ya nuna godiya ga Dr. Matawalle bisa wannan gagarumin taimakon da ya yi.

Ya tabbatar da cewa dukkan waɗanda aka tantance za su karɓi tallafin kamar yadda aka tsara, tare da yin alƙawarin cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da aiki tukuru domin samun nasara a matakai daban-daban a jihar da ƙasa baki ɗaya.

Matawalle ya yi wa Babachir martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi martani ga Babachir Lawal wanda ya riƙe muƙamin sakataren gwamnatin tarayya a mulkin Muhammadu Buhari.

Matawalle wanda ya yi martanin game da takarar Bola Tinubu a 2027, ya bayyana cewa shugaban ƙasan zai zarce kan kujerarsa a wa'adi na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng