Abin da Sanusi II Ya ce kan Kisan ’Yan Arewa a Edo, Ya Yi Addu’o’i ga Kano

Abin da Sanusi II Ya ce kan Kisan ’Yan Arewa a Edo, Ya Yi Addu’o’i ga Kano

  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi Allah wadai da kisan 'yan Arewa da aka yi a jihar Edo, yana mai kira ga hukuma ta bi musu kadunsu
  • Basaraken ya nuna damuwa kan yadda aka yi wa mutanen Bunkure, Garko da Kibiya kisan gilla, yana mai cewa hakan rashin imani ne
  • Sanusi II ya bukaci al'umma su guji jita-jita da daukar doka a hannunsu, su saurari hukuncin hukuma
  • Ya roki Allah ya kare Kano da Najeriya baki ɗaya, yana mai kira ga addu’a domin samun zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan abin da ya faru da yan Arewa a jihar Edo.

Basaraken ya yi Allah wadai da abin da ya faru a garin Uromi da ke jihar bayan kone mafarauta mafi yawansu yan Kano.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda aka yi jana'iza, aka birne ’yan Arewa 16 a Edo cikin hawaye da tausayi

Sanusi II ya magantu kan kisan yan Arewa a Edo
Sarki Sanusi II ya yi Allah wadai da kisan wulakanci da aka yi wa Hausawa a Edo. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi.
Asali: Twitter

Sanusi II ya soki kisan yan Arewa a Edo

Hakan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da Masarautar Kano ta wallafa a shafin X a yau Lahadi 30 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon, Sanusi II ya nuna damuwa kan yadda aka nuna tsantsar rashin imani babu tausayi a harin.

Sarki Sanusi II ya yi kira ga dukan hukumomi da su tsaya domin tabbatar da cewa an bi musu hakkinsu.

Sarki Sanusi II ya ce:

"Muna mika ta'aziyyarmu ga iyalan jama'a sama da 20 mutanen Bunkure da Garko da Kibiya wadanda aka yi wa kisan gilla a jihar Edo.
"Wannan kisan gilla ya tayar mana da hankali ganin yadda aka debi al'umamrmu aka rika jefa su a cikin wuta da ransu.
"Muna kira ga dukkan hukumomi da su tabbatar da cewa an bi musu hakkinsu, muna addu'a Allah ya karbi shahadarsu kuma ya kiyaye afkuwar hakan nan gaba."

Kara karanta wannan

Bayan soke hawa, Sanusi II ya gana da malaman Musulunci da kusoshin gwamnati

Sanusi II ya yi Allah wadai da abin da ya faru da yan Arewa a Edo
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bukaci al'umma su kwantar da hankali kan kisan yan Arewa a Edo. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Asali: Twitter

Edo: Sansui II ya shawarci al'umma

Har ila yau, Sanusi II ya bukaci al'umma da su bar yada jita-jita tare da kiransu da su kwantar da hankalinsu domin jiran hukuncin da za a dauka.

Sarki Sanusi II ya yi addu'a ga masu neman Kano da alheri Ubangiji ya kare su inda ya soki masu neman jihar da sharri da cewa Allah ya mayar musu da sharrinsu.

Ya kara da cewa:

"Muna kira ga al'umma da su kiyayi jita-jita ko daukar doka a hannunsu a zauna lafiya, a saurari hukuncin da hukuma za a ta yi da sakamokon bincike a kan wannan matsala.
"Muna rokon Allah ya ba mu lafiya da zama lafiya, Allah ya tsare mana kasarmu, muna kira ga da su tsananta add'u'a ga kasarmu ta Kano."

Yadda aka birne yan Arewa a Edo

Kun ji cewa rahotanni sun tabbatar da cewa an birne wasu daga cikin yan Arewa da aka hallaka a jihar Edo da ke Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun haɗa kai, sun taso da ƙarfi kan abin da aka yi wa ƴan Arewa a Edo

Garin Udune Efandion a Uromi da ke jihar Edo ya cika da jimami yayin da aka yi jana'izar da birne mutane 16 da aka kashe a ranar Alhamis.

An birne mutum uku a ranar Juma'a 28 ga watan Maris, 2025 yayin da jiya Asabar kuma aka birne 16 cikin jimami.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng