Bidiyon Yadda Aka Yi Jana'iza, Aka Birne ’Yan Arewa 16 a Edo cikin Hawaye da Tausayi
- Garin Udune Efandion a Uromi da ke jihar Edo ya cika da jimami yayin da aka birne mutane 16 da aka kashe a ranar Alhamis
- Aƙalla mutane fiye da 16 da aka kashe kan zarginsu da garkuwa da mutane ba tare da shari’a ko wata kwakkwarar hujja ba
- Wata uwa ta yi kuka tana cewa, “Dana ba mai garkuwa da mutane ba ne' yayin da mahaifin ya rike hotonsa, ya na kuka da alhinin rashi
- An birne mutum uku a jiya Juma'a 28 ga watan Maris, 2025 yayin da yau Asabar kuma aka birne 16 cikin jimami
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uromi, Edo - Ana cikin jimami yayin da aka birne mafarauta da suka gamu da ajalinsu a kan hanyar Port Harcourt zuwa Kano.

Kara karanta wannan
Sanatocin Arewa sun haɗa kai, sun taso da ƙarfi kan abin da aka yi wa ƴan Arewa a Edo
An birne matafiyan ne a garin Udune Efandion da ke Uromi a jihar Edo a yau Asabar 29 ga watan Maris, 2025.

Source: Original
Dattijo ya fadi yadda suka tsira daga kisa
Rahoton Zagazola Makama ya ce mutane na cikin alhini da bakin ciki saboda abin da ya faru inda ya wallafa bidiyon a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan tserewa da wasu suka yi yayin da ake ƙoƙarin kona su a garin Uromi da ke jihar Edo.
Wani dattijo ɗan asalin jihar Kano, Ɗayyabu Yahaya ya yi bayanin yadda aka tare su a Uromi, aka kashe ƴan uwansa a Edo .
Ɗayyabu na ɗaya daga cikin mafarautan da aka tare a Uromi, inda ake zagin mutanen garin sun kashe 16 daga cikinsu.
Dattijon ya ce su 27 suka taso daga Port Harcourt za su dawo Kano kuma ba su gamu da wata matsala ba sai da suka shigo jihar Edo.

Source: Facebook
An yi jana'izar gwarwakin mafarauta a Edo
An hallaka matafiyan ne da aka yi zargin masu garkuwa da mutane, inda fusatattun jama’a suka dauki doka a hannunsu.

Kara karanta wannan
Barau ya yi martani kan kisan 'yan Arewa a Edo, ya fadi hanyar da zai samo musu adalci
Wata uwa ta zauna a gefen kabari, ta na kuka da karfi inda take jimamin mutuwar ɗanta.
Uwar ta ce:
“Dana ba mai garkuwa da mutane ba ne, sai dai kawai ya na wurin da bai dace ba a lokacin da bai dace ba."
Wani mahaifi ya rike hoton dansa guda, yana kallonshi cikin jimami ya ce yaron ya fita da safiya cike da burin rayuwa amma bai dawo ba.
A jiya Juma'a 28 ga watan Maris, 2025, an binne mutum uku, yau kuma Asabar an binne 16.
Yayin da ake zuba kasa na karshe a kaburburan, al’umma suka tsaya shiru, suna tunanin abin da ya faru.
Edo: Gwamnonin Arewa sun soki kisan Hausawa
Kun ji cewa Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da kisan matafiya a Edo, su na cewa wannan abin takaici ne da ya sabawa hakkin dan Adam.
Shugaban gwamnonin kuma Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya ce dole ne a binciki lamarin tare da hukunta masu laifi, domin hana irin haka faruwa a gaba.
Inuwa ya jaddada cewa kowane dan Najeriya na da ‘yancin tafiya ba tare da fargabar farmaki, barazana ko muzgunawa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng