Jajen Peter Obi kan Kisan Ƴan Arewa Ya Bar Baya da Kura, an Bukaci Ya Bar Ɓoye Ɓoye

Jajen Peter Obi kan Kisan Ƴan Arewa Ya Bar Baya da Kura, an Bukaci Ya Bar Ɓoye Ɓoye

  • Jama’a da dama sun caccaki Peter Obi kan bayaninsa game da kisan gilla a Edo, suka ce ya na rage muhimmancin matsalolin da ke shafar Arewa
  • A wata sanarwa, Bashir Ahmad ya ce abin takaici ne yadda Obi ke nuna bangaranci kan abin da ya shafi Arewa, maimakon yin adalci
  • Masu suka sun ce kalaman Obi kamar ya na kare kisan ne, aka ce iyalan mamatan za su ga kamar a bayaninsa ya rage darajar asarar da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Uromi, Edo - Jama’a sun yi ca kan furucin Peter Obi game da kisan gilla a Edo wanda ya jawo maganganu.

Masu suka sun ce Peter Obi yana rage muhimmancin matsalolin da ke shafar Arewacin Najeriya.

An caccaki Peter Obi bayan jajantawa ƴan Arewa da aka kashe a Edo
Bashir Ahmad ya soki salon jajen Peter Obi kan kiran ƴan Arewa a Edo. Hoto: @BashirAhmaad, @PeterObi.
Asali: Twitter

Kisan Hausawa: Bashir Ahmad ya soki Peter Obi

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun haɗa kai, sun taso da ƙarfi kan abin da aka yi wa ƴan Arewa a Edo

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bashir Ahmad ya wallafa a shafin X a yau Asabar 29 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Bashir Ahmad ya ce abin takaici ne yadda Obi ke nuna bangaranci kan abin da ya shafi Arewa.

Ya ce idan har zai goyi bayan kisan ƴan Arewa a Edo gwara ya fito fili madadin kame-kame da yake yi.

Sanarwar ta ce:

“Wannan ne matsala ta da Peter Obi tun da dadewa, duk lokacin da abu ya shafi Arewa, sai ya nemi rage muhimmancinsa ko ya karkatar da hankali.
"A wannan yanayi, ina rahoton kisan ‘yan asalin Edo da ya sa shi gaggauta kiran hukumomi domin tabbatar da adalci ga kowa?
“Mista Obi, babu bukatar juyayi ko sarrafa kalmomi, idan za ka kare irin wannan ta’addanci da rashin imani, ka yi da karfin haka.
"Magana muke yi kan kisar gilla da kona mutum kusan 20 da ransu, ta yaya kake tunanin iyalansu za su ji idan suka karanta bayaninka wanda ke rage girman asarar da suka yi ta hanyar kokarin daidaita lamarin da abin da bai dace ba?”

Kara karanta wannan

Kungiyar Izalah ta yi maganar kisan ƴan Arewa a Edo, ta fadi hanyar dakile lamarin

An taso Peter Obi a gaba kan kisan ƴan Arewa a Edo
Yadda jajen Obi kan kisan ƴan Arewa a Edo ya jawo maganganu. Hoto: Peter Obi.
Asali: Twitter

Rubutun Obi da ya jawo ka-ce-na-ce

Ana zargin Peter Obi ya bukaci hukumomi da su dauki mataki kan kashe-kashen da ake yi a Edo madadin mayar da hankali kan abin da ya faru a jihar.

Obi ya wallafa jajen nasa ne a shafin X inda ya hada jajen da kuma neman a dakile kashe al'ummar Edo da ake yi.

Wasu sun ce sai da rikicin ya kazance ya bukaci adalci sannan ya fito da sanarwa da ke dauke da wasu irin bayanai.

Masu suka sun ce kalaman Obi kamar yana kokarin kare kisan da aka yi wa mutum 20, sun ce bai yi tir da lamarin ba yadda ya kamata.

Hakan zai sa iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu su ga kalaman Obi sun rage darajar asarar da suka yi.

Izalah ta yi Allah wadai da kisan Hausawa

Kun ji cewa ƙungiyar Izalah a Najeriya ta yi Allah wadai da kisan wasu matafiya ƴan Arewa a jihar Edo da ke yankin Kudu maso Kudu.

Shugaban kungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ya bayyana haka, a nan ne ya bukaci hukunta waɗanda suka aikata laifin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng