Fubara: An 'Gano' Shirin Tinubu kan Gwamnonin da ba Su Goyon Bayansa a 2027
- Tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi ya ce dokar ta-baci da Bola Tinubu ya kafa a jihar yunkuri ne na tsoratar da gwamnonin da ba za su mara masa baya ba
- Shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamna Simi Subara, mataimakiyarsa, da ’yan majalisar dokokin Ribas har na tsawon wata shida bisa dalilin rikicin siyasa
- Amaechi ya ce Fubara ba shi da alhakin tsaro a Rivers, kuma ana hukunta shi ne saboda wani laifi da bai aikata ba musamman da ke da alaka da zaben 2027
- Tsohon ministan sufurin wanda ya yi gwamna a baya, ya bukaci al’ummar Rivers su bijirewa wannan doka ta hanyar yin zanga-zanga ta dimokuradiyya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya yi magana kan sanya dokar ta-ɓaci a Rivers da Bola Tinubu ya yi.
Amaechi ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da dokar ta-baci a jihar don tsoratar da gwamnonin da ba za su goyi bayansa ba a 2027.

Asali: Twitter
Yadda aka saka dokar ta-ɓaci a Rivers
Amaechi ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da ƴan jaridu ranar Juma’a 28 ga watan Maris, 2025, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar 18 ga watan Maris, Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Rivers, yana mai cewa rikicin siyasa da lalata kayan hako mai ne dalilin daukar matakin.
Shugaban kasa ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukan ’yan majalisar dokoki na tsawon wata shida.
Tinubu ya kuma nada Ibok-Ete Ibas a matsayin mai kula da jihar wanda zai shafe watanni a ragamar mulki kafin sanin matakin da ya kamata a dauka.
Wannan mataki ya fuskanci suka daga jam’iyyun adawa, kungiyoyin farar hula, da Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), wadanda suka ce ba bisa doka aka yi hakan ba.

Kara karanta wannan
Ribas: Tambuwal ya tona yadda aka yi watsi da doka a majalisa don biyan buƙatar Tinubu

Asali: Facebook
Amaechi ya kare Fubara kan rigimar siyasar Rivers
A ɓangarensa, Amaechi ya ce abin takaici ne inda ya ce dakataccen gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara ba shi da alaka da rigimar jihar.
Amaechi ya ce:
"Idan ba a yi taka-tsantsan ba, shugaban kasa zai iya cire kowa daga mukaminsa.
"Gwamnan Rivers ba shi da alhakin tsaro, me ya sa za a hukunta wanda bai aikata laifi ba?"
Ya bukaci jama’ar Rivers da su yi zanga-zanga ta lumana don nuna adawa da wannan doka saboda neman ƴancinsu kan rigimar da ke wakana a jihar.
Amaechi ya fadi dalilinsa na shiga siyasa
Mun ba ku labarin cewa tsohon Ministan Sufuri a gwamnatin tarayya, Rotimi Amaechi, ya bayyana dalilin fadawarsa cikin siyasa ba ji ba gani tun shekaru da dama da suka wuce.
Rt. Hon. Amaechi ya bayyana cewa talauci ne ya sa ya tsaya tsayin daka a siyasa tun bayan kammala jami'a a shekarar 1987 wanda har yanzu yake cikinta tsundum.
Tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa ‘yan siyasa a Najeriya suna amfani da mukamansu ne don sata, cin zarafi, da kuma riƙe mulki ta kowace hanya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng