Rikicin Rivers: Tsohon Gwamna Ya Fasa Kwai, Ya Fadi Dalilin Rigimar Wike da Fubara
- Tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi ya taɓo batun rikicin siyasar da ya daɗe yana addabar jihar mai arziƙin mai
- A cewar Amaechi taƙaddamar da ake yi tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike ta samo asali ne sakamakon rabon kuɗi jihar
- Ya kuma soki shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan dokar ta ɓacin da ya ayyana a jihar tare da dakatar da Gwamna Fubara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan rikicin da ke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike.
Rotimi Amaechi ya bayyana cewa rikicin da ke tsakanin gwamnan na jihar Rivers da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya na da alaƙa da rabon kuɗin jihar.

Asali: UGC
Rotimi Amaechi ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da aka yi da shi a tashar DW Africa a ranar Juma'a, 28 ga watan Maris 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Amaechi ya ce kan rikicin Rivers?
Tsohon gwamnan ya kuma ce dokar ta ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya kafa a jihar ta saɓawa kundin tsarin mulki.
"Rigimar da ke tsakanin gwamnan jihar Rivers na yanzu da ministan birnin tarayya Abuja, tana da alaƙa da rabon kuɗi. Idan ba haka ba, mene ne dalilin rikicin?"
"Yanzu ƴan Najeriya sun daina ƙin jinin cin hanci da rashawa. Ban ga wani a tituna yana tambayar menene matsalar ba. Shin su duka biyun za su iya fitowa su gayawa jama’a gaskiyar abin da ke faruwa?"
"Yanzu an hana mu dimokuradiyya. Jihar Rivers ce kawai jiha ɗaya tilo a ƙasar nan da ba ta samun romon dimokuraɗiyya a halin yanzu. Sun tilasta mana mulkin soja."
"Abu na biyu, shugaban ƙasa ya saɓa da kundin tsarin mulki. Sashe na 188 ya bayyana hanyoyin da gwamna zai iya barin muƙaminsa, ko dai ta mutuwa, murabus, ko tsige shi."
"Bai ce watarana kawai za a tashi da safe, sai a ce wani mutum mai suna shugaban Najeriya ya koreka daga ofis ba, wanda hakan yana haifar da koma baya ga dimokuraɗiyya."
- Rotimi Chibuike Amaechi
Amaechi ya nuna yatsa ga Tinubu
Tsohon ministan sufurin ya jaddada cewa shugaban ƙasa yana da hannu a rikicin jihar Rivers saboda yana son samun ƙarfin iko don hamɓarar da gwamnoni da ba za su mara masa baya ba a zaɓen 2027.
"Jita-jita sun yadu cewa idan wani gwamna bai yi taka-tsantsan ba, shugaban kasa zai cire shi. Don haka, matsalar jihar Rivers ta shafi rabon kuɗi da siyasar 2027."
- Rotimi Chibuike Amaechi
Wike ya faɗi dalilin ƙwace filin PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya musanta cewa saboda dalilai.na siyasa aka ƙwace filin jam'iyyar PDP.
Wike ya bayyana cewa an ƙwace takardun mallakar filin ne saboda jam'iyyar ta kasa biyan kuɗin haraji na tsawon shekaru masu yawa.
Asali: Legit.ng