Barau Ya Yi Martani kan Kisan 'Yan Arewa a Edo, Ya Fadi Hanyar da Zai Samo Musu Adalci

Barau Ya Yi Martani kan Kisan 'Yan Arewa a Edo, Ya Fadi Hanyar da Zai Samo Musu Adalci

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya nuna takaicinsa kan kisan da aka yi wa ƴan Arewa a jihar Edo
  • Barau ya yi Allah da kisan gillar, inda ya buƙaci jami'an tsaro da su tabbatar da cewa sun zaƙulo miyagun da suka aikata laifin
  • Ya buƙaci jama'a da su kwantar da hankulansu, ya ba da tabbacin mutanen da suka aikata laifin za su girbi abin da suka shuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yi magana kan kisan da aka yi wa wasu matafiya ƴan Arewa a jihar Edo.

Sanata Barau Jibrin ya yi Allah wadai da kisan wanda aka yi a garin Uromi, ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta jihar Edo, yana mai kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta kamo masu laifin.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun haɗa kai, sun taso da ƙarfi kan abin da aka yi wa ƴan Arewa a Edo

Barau ya soki kisan 'yan Arewa a Edo
Barau ya yi Allah wadai da kisan 'yan Arewa a Edo Hoto: @baraujibrin
Asali: Facebook

Sanata Barau ya bayyana hakan ne a wanu rubutu da ya yi a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu gungun jama’a sun tare matafiyan da galibinsu mafarauta ne waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, da ke hanyarsu ta komawa Kano don shagulgulan Sallah, inda suka farmake su, suka bincike motarsu, sannan suka cinna musu wuta.

Me Sanata Barau ya ce kan kisan ƴan Arewa?

Sanata Barau ya bayyana wannan kisan a matsayin dabbanci, rashin imani, da ta’addanci, yana mai roƙon rundunar ƴan sandan jihar Edo da sauran hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu, yana tabbatar da cewa waɗanda suka aikata wannan ta’asa za su fuskanci hukuncin da ya dace da su.

Ya bayyana shirinsa na gabatar da ƙudiri a majalisar dattawa domin tabbatar da cewa an hukunta masu hannu a mummunan kisan.

Kara karanta wannan

Kungiyar Izalah ta yi maganar kisan ƴan Arewa a Edo, ta fadi hanyar dakile lamarin

Sanata Barau Jibrin
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin Hoto: @barauijibrin
Asali: Twitter
"Na samu kiran waya daga mazaɓata ta da kuma sauran ƴan Najeriya dangane da wannan kisan gilla da aka yi wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a jihar Edo."
"Na yi Allah wadai ɗari bisa ɗari da wannan ta’asa da aka aikata kan ƴan Najeriyan da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba."
"Ina kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki wajen cafke waɗannan mugayen mutane tare da tabbatar da cewa an hukunta su bisa laifukan da suka aikata."
"Najeriya kasa ce da ke da kabilu daban-daban. Saboda haka, dole ne mu rungumi juna a matsayin ƴan uwa domin samun ci gaba da bunƙasar ƙasarmu."

Sanata Barau ya yi addu’a domin neman rahama ga waɗanda aka kashe, tare da yin kira ga iyalansu da su kwantar da hankalinsu, ya na mai tabbatar da cewa gwamnati za ta tabbatar an yi musu adalci.

Kara karanta wannan

"Abin tausayi": An ji ainihin yadda aka kashe ƴan Arewa a jihar Edo, mutum 5 suka tsira

Izala ta magantu kan kisan ƴan Arewa a Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Izala ta yi Allah wadai kan kisan da aka yi wa wasu matafiya ƴan Arewa a jihar Edo.

Ƙungiyar Izala ta yi kira ga hukumomi kan su tabbatar da cewa sun gudanar da sahihin bincike domin zaƙulo masu hannu a lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng