'Yan Bindiga Sun Shiga Mummunan Yanayi bayan Haukacewa saboda Shan Kwaya

'Yan Bindiga Sun Shiga Mummunan Yanayi bayan Haukacewa saboda Shan Kwaya

  • Wasu jagororin ‘yan bindiga uku sun haukace a dazukan da ke yankin Zamfara, lamarin da ya haddasa rudani a cikin dabarsu
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa 'yan uwansu sun kwace makamansu bayan faruwar lamarin, aka bar su suna yawo a daji
  • Ana hasashen cewa yawan shan miyagun kwayoyi da 'yan ta'addan ke yi ne ya haddasa musu ciwon haukar da suke fama da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Rahotanni daga Zamfara sun nuna cewa wasu shahararrun shugabannin ‘yan bindiga uku da suka dade suna ta’addanci sun haukace ba zato ba tsammani.

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya haifar da rudani a tsakanin mayakan su, inda suka kwace makaman da suke dauke da su.

Yan bindiga
Jagororin 'yan bindiga sun haukace a Zamfara. Hoto: Zagazola Makama
Asali: Twitter

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa lamarin ya faru ne a ranar 27 ga Maris, 2025, kuma hakan ya haddasa fargaba a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Lauya ya mika bukatu 7 ga Bola Tinubu da gwamna kan kisan Hausawa a Edo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindigar da suka haukace a Zamfara

Daya daga cikin shugabannin da suka haukace shi ne Kachalla Dan Baba, wanda ke da babbar mafaka a kauyen Kudo, kusa da dajin Buzaya a karamar hukumar Maru.

Dan Baba ya na da fiye da mayaka 50 karkashinsa, kuma ya dade yana jagorantar satar mutane, kwace dabbobi da kuma hare-haren kan tituna.

Shi kuwa Kachalla Abu Guddi ya kasance jagoran hare-haren ta’addanci a kauyen Gidan Garba, ana zarginsa da yin kisan gilla da safarar makamai.

Isuhu
Jagoran 'yan bindiga, Kachalla Isuhu da aka kashe a Zamfara. Hoto: Abdulaziz Abdulaziz
Asali: Facebook

Na uku shi ne Kachalla Bello Kurma, wanda ke da sansani a dajin Buzaya, daya daga cikin mafakar ‘yan bindiga a yankin Maru.

An bayyana shi a matsayin daya daga cikin shugabannin ‘yan bindiga mafiya hadari a yankin, tare da alaka da wasu kungiyoyin ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma.

Yadda aka gano 'yan bindigan sun haukace

Kara karanta wannan

An fara kama mutanen da suka kashe 'yan Arewa a Edo

Wani mafarauci da ke bibiyar ayyukan ‘yan bindiga a yankin ya bayyana cewa shugabannin uku sun fara nuna alamun hauka, ciki har da magana da kansu,

Haka kuma ya bayyana cewa ana ganinsu suna sumbatu da kuma daukar matakan da ba su da ma’ana.

A cewarsa:

“Yan bindigar shugabanni ne da ake tsoro, amma kwatsam sai suka haukace.
Da mayakansu suka ga alamun haukar, sun kwace makamansu suka bar su a cikin daji.”

Bayan wannan lamari, ana rade-radin cewa kungiyoyin ‘yan bindigar za su rarrabu ko kuma su shiga sababbin kawance domin ci gaba da ayyukansu.

Me ya haddasa haukar 'yan bindiga?

Ana hasashen cewa yawan shan miyagun kwayoyi na iya zama daya daga cikin dalilan da suka haddasa haukar 'yan ta'addan.

Baya ga haka, wasu al’ummomi na ganin cewa wata azaba daga Allah ce ko kuma sakamakon addu’o’in al’umma na neman kawo karshen ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo

An kashe 'yan Arewa a jihar Edo

A wani rahoton, kun ji cewa wasu matasa a jihar Edo sun kashe matafiya da suka fito daga Fatakwal zuwa Arewacin Najeriya.

Kisan matafiyan ya jawo Najeriya ta dauki zafi, kuma shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci jami'an tsaro su gaggauta daukar mataki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng