A karshe, Shugaba Tinubu Ya Yi Maganar Kisan da Aka Yi Wa Ƴan Arewa a Jihar Edo
- Bola Ahmed Tinubu ya yi tir da kisan gillar da aka yi wa matafiya 16 a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a Edo
- Mai girma Tinubu ya umarci ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike mai zurfi tare da kama waɗanda suka aikata kisan
- Shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan waɗanda lamarin ya shafa kuma ya ba su tabbacin cewa jinin ƴan uwansu ba zai zuba a banza ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu mafarauta da ke kan hanyar zuwa Kano a jihar Edo.
An tattaro cewa an kashe mafarautan ƴan Arewa a lokacin da wasu ‘yan sintiri suka tsare su a garin Uromi, karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta jihar Edo.

Kara karanta wannan
"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo

Asali: Twitter
Edo: Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai
Bola Tinubu ya yi tir da kisan matafiyan ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X a daren ranar Juma'a, 28 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya bayyana matukar bakin cikinsa kan wannan danyen aiki da ake zargin mutanen gari sun aikata a jihar Edo.
Tinubu ya buƙaci jami'an tsaro su yi bincike
Ya kuma umarci ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi da gaggawa don gano wadanda suka aikata wannan ta’asa tare da hukunta su.
Shugaban kasa ya jajanta wa iyalan mamatan, ya na mai tabbatar musu da cewa ba za a bar bata-gari su ci gaba da zubar da jinin bayin Allah ba.
Tinubu ya kuma jaddada cewa dokar kasa ba ta yarda da daukar doka a hannu ba, kuma kowa na da ‘yancin yin rayuwa da tafiye-tafiye a ko’ina cikin Najeriya ba tare da tsangwama ba.
"Ɗaukar doka a hannu ba shi da matsuguni a Najeriya kuma kowane ɗan ƙasa ya na da ƴancin yin tafiye-tafiya zuwa ko'in ba tare da tsangwama ba," in ji Tinubu.
Shugaban ƙasa ya yabawa gwamnan Edo
Bugu da kari, Tinubu ya jinjinawa Gwamnan Edo, Sanata Monday Okpebholo, da shugabannin al’umma a Uromi bisa yadda suka dauki matakin gaggawa don hana tayar da tarzoma.
Tun farko dai Gwamna Okpebholo ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin, kuma rahotanni sun nuna har an kama wasu daga cikin waɗanda suka yi kisan.
Hakan ya sa shugaban kasa ya yabi mai girma gwamna tare da jinjina masa bisa namijin kokarin da ya yi musamnan wajen dakile faruwar tashin hankali bayan lamarin.
Pantami ya ba da mafita kan kisan Edo
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya ce bidiyon kisan matafiya ya nuna irin rashin imanin waɗanda suka yi aika-aikar.
Farfesa Pantami ya ba hukumonin tsaro shawarin hanyoyin da za su bi wajen kamo masu hannu a kisa ta hanyar amfani da fasahohin zamani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng