Sheikh Pantami Ya Jero Hanyoyi 3 da Za a Kama Waɗanda Suka Kashe Ƴan Arewa a Edo

Sheikh Pantami Ya Jero Hanyoyi 3 da Za a Kama Waɗanda Suka Kashe Ƴan Arewa a Edo

  • Babban malamin addini, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana damuwa kan kisan gilla da aka yi wa wasu matafiya 16 ƴan Arewa a jihar Edo
  • Tsohon ministan sadarwa ya ce bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna rashin imani da zaluncin da aka yi wa bayin Allah
  • Ya bukaci hukumomin tsaro su gudanar da bincike domin kamo masu hannu a lamarin, ya jero fasahohin zamanin da yake ganin za su taimaka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya bayyana bacin ransa kan kisan gillar da aka yi wa mutum 16 da ba su ji ba, ba su gani ba a Udune Efandion da ke Uromi, Jihar Edo.

A cewarsa, wannan lamari ne da ya nuna rashin imani da tauye hakkin dan Adam, kuma ya nuna illar ɗaukar doka a hannu.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun haɗa kai kan kisan Hausawa a Edo, sun shawarci al'umma

Pantami.
Pantami ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa matafiya 16 a Edo Hoto: Prof. Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Sheikh Isa Pantami ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Juma'a, 28 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Pantami ya nuna ɓacin ransa

Pantami ya ce bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna irin rashin tausayi da zaluncin da aka aikata wa wadannan mutane.

Ya kara da cewa hakkin gwamnati ne ta kare rayukan al’ummarta kuma ta tabbatar da cewa an hukunta masu aikata laifi ba tare da son rai ba.

Taohon ministan ya ce:

“Ana cewa rashin adalci a ko ina barazana ce ga adalci a ko’ina. Kare rayukan ‘yan kasa da dukiyoyinsu ba alfarma ba ce, a’a, hakki ne da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tabbatar a karkashin sashe na 14 (2) (b).”

Pantami ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan wannan kisa ta amfani da fasahar zamani.

Kara karanta wannan

Atiku ya bi layin Kwankwaso game da mummunan kisan da aka yi wa ƴan Arewa a Edo

Ta wane hanyoyi za a kama makasan?

Ya bada shawarar amfani da wasu hanyoyin fasaha don gano wadanda suka aikata wannan laifi, kamar:

1. Fasahar gano abubuwa (Object Detection) – Ana iya amfani da fasahar hange na kwamfuta kamar OpenCV da PyTorch don gano fuska, fata, tufafi ko wasu kayan mutane a bidiyon.

2. Fasahar gane fuska (FRT) – Ana iya amfani da fasahar AI kamar Convolutional Neural Networks da OpenFace don kwatanta fuskar wadanda ke cikin bidiyon da wadanda ake zargi.

3. Nazarin bidiyo ta hanyar Deep Learning – Ana iya amfani da Google Cloud Video Intelligence don nazarin cikakken bayani daga bidiyon da ke yawo.

Ya ce wadannan fasahohi na zamani za su taimaka wajen gano wadanda suka aikata wannan ta’asa da ma wadanda suka aikata irin ta a baya ko masu shirin aikatawa a nan gaba.

Malam Pantami.
Sheikh Pantami ya jero hanyoyi 3 da za a kama waɗanda suka kashe yan Arewa a Edo Hoto: Prof. Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Sheikh Pantami ya yi wa mamatan addu'a

Kara karanta wannan

Kano: Abin da Reno Omokri ya ce bayan ƙone Hausawa a Edo, ya shawarci ƴan Arewa

A karshe, Pantami ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, yana mai rokon Allah ya jikansu da rahama, ya kuma kawo zaman lafiya a Najeriya.

Ya kuma roki Allah ya tona asirin duk masu aikata irin wannan danyen aiki a Najeriya da duniya baki daya.

Atiku ya yi Allah wadai da kisan Edo

A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya bi sahun Rabiu Kwankwaso, ya bukaci a binciko duk wani mai hannu a kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewa a jihar Edo.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da duka wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan mummunan lamari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel