Hawan Sallah: Sheikh Ibrahim Khalil Ya Magantu kan Matakin Aminu Ado a Kano

Hawan Sallah: Sheikh Ibrahim Khalil Ya Magantu kan Matakin Aminu Ado a Kano

  • Ibrahim Khalil ya yaba wa Aminu Ado Bayero kan janye shirinsa na hawan Sallah, ya na mai cewa zaman lafiya ya fi komai muhimmanci
  • Ya ce matakin Sarkin Kano na 15 ya dace da maslahar tsaro kuma ya nuna cancantarsa a shugabanci
  • Sheikh Khalil ya bukaci shugabanni su fifita zaman lafiya, ya na mai cewa babu mulki mai amfani idan babu kwanciyar hankali
  • Malamin ya roki Allah ya kawo zaman lafiya da wadata, ya na mai tuna irin kokarin da marigayi Ado Bayero ya yi a baya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sheikh Ibrahim Khalil ya magantu bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya janye shirinsa na hawan sallah.

Shehin malamin ya yabawa basaraken inda ya ce babban abin a yaba ne duba da yadda ya kula da maslahar tsaro kan komai.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya jero hanyoyi 3 da za a kama waɗanda suka kashe yan Arewa a Edo

Sheikh Khalil ya yi magana bayan Aminu Ado ya janye hawan sallah a Kano
Sheikh Ibrahim Khalil ya yabawa Aminu Ado Bayero bayan janye hawan sallah a Kano. Hoto: Khalil Network, Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Ibrahim Khalil ya yabawa Aminu Ado Bayero

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Khalil Network ya wallafa a manhajar Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon, Sheikh Khalil ya ce Aminu Ado ya cancanci yabo kan daukar wannan mataki da ya yi.

Malamin ya yabawa marigayi tsohon Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero kan son zaman lafiya da ya nuna yayin mulkinsa.

Malamin ya ce:

"Du lokacin aka wayi gari wani mutum bai marawa lafiya da zaman lafiya baya ba, to wannan mutum ya nuna bai fahimci rayuwa ba.
"Yau kuma wajibi ne a yabawa Sarki na 15 a jerin sarakunan Kano na Fulani da ya ce ya janye hawan da a baya ya yi niyar yi.
"Kuma ya ga cewa janyewar ya fi alheri saboda Kano da mutanen jihar da Arewa da kuma mutanen Najeriya, kuma saboda ragowar al'ummar duniya da suke son kwanciyar hankali."

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun haɗa kai kan kisan Hausawa a Edo, sun shawarci al'umma

Shehin malami ya yaba Aminu Ado Bayero a Kano
Sheikh Ibrahim Khalil ya yabawa Aminu Ado Bayero bayan janye hawan sallah a Kano. Hoto: Masarautar Kano.
Asali: UGC

Sheikh Ibrahim Khalil ya shawarci shugabanni

Sheikh Khalil ya ce akwai bukatar shugabanni su fi ba zaman lafiya fifiko saboda kowane mulki idan babu zaman lafiya ba komai ba ne.

Daga bisani ya roki Allah ya samar da kwanciyar hankali da zaman lafiya da wadata a tsakanin al'umma.

Ya kara da cewa:

"Haka ake bukatar shugabanni su fahimci zaman lafiya shi ne kan gaba ba komai na mulki ba, domin duk mulkin da babu zaman lafiya bai cika mulki ba.
"Ina rokon Allah ya bamu kwanciyar hankali da tsawon rai da lafiya da kuma wadata Allah ya sa mutane su fahimci zaman lafiya shi ne rayuwa."

Shehin malamin ya tuno irin gudunmawar da marigayi tsohon Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya bayar game da zaman lafiya.

'Yan sanda sun hana hawan sallah a Kano

Kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta sanar da haramta duk wani hawan Sallah a bukukuwan sallah karama, domin tabbatar da doka da oda.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Aminu Ado ba zai taba iya gudanar da hawan sallah a Kano ba'

Kwamishinan 'yan sanda na Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne saboda karuwar rashin jituwa a jihar.

Bakori ya gargadi Musulmi da su bi dokokin tsaro, ciki har da guje wa tukin ganganci da hawan doki, tare da kiyaye sharudan da aka gindaya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng