Rigimar Gide da Aliero Ta Rikice bayan Kisan Rikakken Ɗan Bindiga, An Kira Taron Gaggawa

Rigimar Gide da Aliero Ta Rikice bayan Kisan Rikakken Ɗan Bindiga, An Kira Taron Gaggawa

  • Rikakken ɗan bindiga, Ado Aliero, ya kira taron gaggawa bayan kashe ɗan uwansa, Isuhu Yellow, da yaran Dogo Gide suka yi a Zamfara
  • Wata majiya ta tabbatar da cewa an gudanar da taron ne a sansanin Aliero da ke dajin Munhaye, ƙaramar hukumar Tsafe a jiya Alhamis
  • Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa an ga ɗaruruwan ‘yan bindiga a babura suna tafiya zuwa Munhaye don halartar taron da Aliero ya kira
  • Ana zargin kashe Isuhu Yellow wata alama ce ta rikicin da ke tsakanin Aliero da Gide, wanda ke haddasa tashin hankali da asarar rayuka a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Shugaban ‘yan bindiga da ya yi kaurin suna, Ado Aliero, ya kira taron gaggawa na ƴan ta'adda a Zamfara.

An ce Aliero ya kira taron ne tare da mayakansa da magoya bayansa bayan kashe ɗan uwansa wanda rikakken dan bindiga ne, Isuhu Yellow.

Kara karanta wannan

An kona 'yan Arewa kurmus suna dawowa gida hutun sallah a jihar Edo

An yi taron gaggawa bayan kisan rikakken dan bindiga a Zamfara
Ado Aliero ya kira taron gaggawa bayan kisan ɗan uwansa. Hoto: Legit.
Asali: Original

Jami'an tsaro sun hallaka ɗan bindiga, Isuhu

Rahoton Zagazola Makama ya ce ana zargin ‘yan bindigar Dogo Gide ne suka kashe ɗan uwansa, Ɗan-Isuhu Yellow.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan rahotanni sun yi nuni da cewa jami’an tsaro sun yi nasarar hallaka fitaccen ɗan ta’adda Ɗan-Isuhu wanda ya addabi al’ummar Zamfara da Katsina.

An tabbatar da mutuwar Dan-Isuhu, wanda yake dan uwa ga Ado Aliero, bayan wata fafatawa mai zafi da jami’an tsaro suka yi da shi.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa Ɗan-Isuhu ya kasance sanannen jagoran ayyukan ta’addanci da suka hada da kisan jami’an tsaro da satar mutane.

Ado Aliero ya kaɗu da kisan Ɗan-Isuhu

Wata majiya ta shaida cewa an gudanar da taron da Aliero ya kira ne ranar Alhamis 28 ga watan Maris, 2025.

An gudanar da taron ne a ɗaya daga cikin sansanonin Aliero da ke dajin Munhaye a karamar hukumar Tsafe da ke Zamfara.

Kara karanta wannan

An hallaka Kachalla Dan Isuhu da ya sa haraji a kauyuka 21 ya kashe Farfesa Yusuf

Majiyar ta ce:

“Mun ga ɗaruruwan ‘yan bindiga a babura su na fitowa daga sassa daban-daban, suna nufin Munhaye."
An hallaka rikakken dan bindiga a Zamfara
Ado Aliero ya kira taron gaggawa bayan kisan ɗan uwansa, Kachallah Isuhu Yellow. Hoto: Abdulaziz Abdulaziz.
Asali: Facebook

Ana ci gaba da rigima Aliero da Gide

Majiyar da ta nemi a ɓoye sunanta ta ce hakan bai rasa nasaba da kisan rikakken dan bindiga, Ɗan-Isuhu Yellow.

Ana ganin kisan Isuhu Yellow a kauyen Dan Jibga a matsayin ɓangare na rikicin Aliero da Gide, manyan shugabannin ‘yan bindiga da ke ta'adi a Arewa maso Yamma.

Majiyoyi sun ce an kira taron ne domin tattauna martani da dabarun da za a ɗauka bayan harin da aka kai.

Rikicin Aliero da Dogo Gide ya haddasa hare-hare da asarar rayuka, inda aka tilasta wa al’ummomi da dama yin gudun hijira a Zamfara da wasu jihohi.

Sojoji sun cafke hadimin ɗan bindiga

Kun ji cewa rundunar tsaro sun ƙara ƙaimi wajen farautar shugaban ƴan bindiga, Kachalla Dan Mai Kinni, bayan cafke abokinsa Lawali Malangaro.

Rahotanni sun nuna cewa Malangaro, ɗan asalin Tsibiri, an kama shi ne a Galadi ta hannun 'yan sa-kai da ke yaki da ƴan bindiga a Zamfara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng