"Mun Hango Babbar Barazana," Yan Sanda Sun Hana Hawan Sallah a Kano

"Mun Hango Babbar Barazana," Yan Sanda Sun Hana Hawan Sallah a Kano

  • Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta sanar da haramta duk wani hawan Sallah a bukukuwan sallah karama, domin tabbatar da doka da oda
  • Kwamishinan 'yan sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne saboda karuwar rashin jituwa a jihar
  • Bakori ya gargadi musulmi da su bi dokokin tsaro, ciki har da guje wa tukin ganganci da hawan doki, tare da kiyaye dokar da aka gindaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Rundunar yan sandan jihar Kano ta hana duk wani hawan Sallah yayin bukukuwan sallah karama da ke tunkara wa.

Rundunar ta bayyana cewa an dauki matakin haramta hawan ne domin tabbatar da doka da oda, bayan ta samu bayanan sirri a kan batun.

Kara karanta wannan

An fara kama mutanen da suka kashe 'yan Arewa a Edo

Jihar
An hana hawan Sallah a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa/Sanusi II Dynasty
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kwamishinan ‘yan Sanda na Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya sanar da hakan yayin tattauna wa da yan jarida a ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin hana hawan sallah a Kano

Intel region ta ruwaito kwamishinan ‘yan sandan na cewa binciken tsaro ya nuna cewa akwai karuwar rashin jituwa da kuma barazanar da ke tattare da hawan Sallah, wanda ka iya haddasa tashin hankali.

CP Ibrahim Adamu Bakori ya ce:

“Bayan samun sahihan bayanan sirri kan shirin wasu bata-gari da masu daukar nauyinsu na yin amfani da hawan Sallah domin haddasa tarzoma, rundunar, tare da hadin gwiwar gwamnatin Kano da sauran masu ruwa da tsaki, ta yanke hukuncin hana hawan sallah a fadin jihar."

Kwamishinan ya tabbatar wa da mazauna Kano cewa an dauki matakan tsaro don kare lafiyar masu zuwa Sallar Idi a wuraren da aka kebe domin yin ibada.

‘Yan sanda sun ja kunnen mazauna Kano

Kara karanta wannan

"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo

CP Ibrahim Adamu Bakori ya bukaci musulmi su bi dokokin tsaro, ciki har da guje wa hana hawan doki wato Kilisa, tseren motoci, tukin ganganci da sauransu.

Haka kuma, ya gargadi iyaye da masu kula da yara da su hana ‘ya’yansu shiga hannun bata-gari, tare da kiyaye doka da oda domin hana tashin hankali.

Jihar
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Ya ce:

“Yayin da muke bukukuwa, dole ne mu tuna cewa zaman lafiya shi ne ginshikin rayuwa. Dole mu manta da sabaninmu mu hada kai a matsayin ‘yan kasa masu bin doka don cigaban jiharmu da kasa baki daya.”

Ana neman hadin kai a Kano

Rundunar ‘yan sanda ta bukaci ci gaba da hadin gwiwa da hukumomin tsaro tare da kira ga mazauna Kano da su rika kai rahoton duk wani motsi da ba su aminta da shi ba ga jami'an tsaro.

Wannan matakin na zuwa ne bayan da Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da janye shirin gudanar da hawan Sallah domin tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya jero hanyoyi 3 da za a kama waɗanda suka kashe yan Arewa a Edo

Kano: Aminu Ado ya janye hawan sallah

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kawo karshen jita-jitar da ta dauki hankalin mazauna jihar kan batun hawan Sallah guda biyu yayin karamar sallah.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa an dakatar da dukkan shirye-shiryen da fadarsa ta yi na gudanar da hawan bukukuwan Karamar Sallah a jihar Kano saboda tsaron rayukan jama'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng