Kano: Abin da Reno Omokri Ya ce bayan Ƙone Hausawa a Edo, Ya Shawarci Ƴan Arewa

Kano: Abin da Reno Omokri Ya ce bayan Ƙone Hausawa a Edo, Ya Shawarci Ƴan Arewa

  • Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri, ya yi Allah wadai da kisan matafiya 'yan Arewa a Edo, ya na mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici
  • Omokri ya nuna damuwa kan yadda wasu ke daukar doka a hannunsu ba tare da tsoron hukunci ba, yana mai bukatar hukunta wadanda suka aikata kisan
  • Ya bukaci gwamnatin Edo da ta dauki mataki, tare da jaddada cewa rayuwar dukkan 'yan Najeriya na da mahimmanci ba tare da la'akari da yanki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Benin-City, Edo - Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya yi Allah wadai da abin da ya faru da ƴan Arewa a jihar Edo.

Omokri ya nuna damuwa kan yadda mutane ke ɗaukar doka a hannunsu ba tare da tsoron abin da ka iya zuwa ya dawo ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi magana da aka yi wa ƴan Arewa kisan 'wulakanci' a jihar Edo

Omokri ya yi magana bayan kisan ƴan Kano a jihar Edo
Reno Omokri ya shawarci ƴan Arewa su kai zuciya nesa kan abin da ya faru a Edo. Hoto: Reno Omokri.
Asali: Facebook

Reno Omokri ya kaɗu da kisan ƴan Arewa

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Omokri ya wallafa a shafin X a yau Juma'a 28 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fitaccen mai sharhi, Reno Omokri, ya soki kisan wasu matafiya da ake zargin suna kan hanyarsu daga Port Harcourt zuwa Kano don hutun Sallah.

Ya ce abin bai dace ba kuma abin bakin ciki ne duba da yadda mutanen suka dauki doka a hannunsu ba tare da bincike ba.

Omokri ya bukaci gwamnatin Edo da ta dauki matakin gaggawa domin hukunta masu hannu a lamarin.

Ya jaddada cewa rayuwar ’yan Najeriya na da muhimmanci ba tare da la’akari da bambancin yanki ba.

Reno Omokri ya roki ’yan Arewa da su kwantar da hankalinsu, ya na mai cewa yana da kwarin gwiwa cewa Bola Tinubu zai dauki mataki idan Edo ta kasa yin abin da ya dace.

Kara karanta wannan

An kona 'yan Arewa kurmus suna dawowa gida hutun sallah a jihar Edo

"Tun da wannan abu ya faru a Jihar Edo, ina kira ga Gwamnatin Edo da ta gaggauta daukar mataki domin hukunta duk masu hannu a lamarin, akwai bukatar a samar da adalci cikin gaggawa.
"Ina rokon Mutanen Arewa da su kwantar da hankalinsu domin a ba wa Gwamnatin Edo lokaci ta yi abin da ya dace."
Yadda wasu suka koma ƴan Arewa kurmus a Edo
Reno Omokri ya soki daukar doka a hannu bayan kisan ƴan Arewa a Edo. Hoto: Sen. Monday Okpebholo.
Asali: Twitter

Kalubalen da Omokri ya jefa ga ƴan Arewa

A karshe, ya kalubalanci fitattun mutane da ke yawan magana kan abin da ke faruwa a Arewa amma suke shiru idan irin hakan ya faru a Kudu.

Ya bukaci da su fito fili su goyi bayan neman adalci domin nuna cewa suna tare da kowa.

"Ina mika ta'aziyyata ga iyalan waɗanda abin ya shafa, musamman ga gwamnati da al'ummar jihohin da mamatan suka fito."
"A ƙarshe, ina kira ga waɗanda ke da karfin murya idan abu ya faru a Arewa amma suke yin shiru idan irin hakan ya faru kusa da su.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Dalung ya yi gargadi kan 'shirin' saka dokar ta baci a Kano

"Su fito su nuna cewa su na tare da kowa ta hanyar goyon bayan neman adalci ga 'yan uwanmu da aka kashe cikin yanayi na tashin hankali."

Yadda aka kona ƴan Arewa a Edo

Kun ji cewa wasu matasa sun kashe matafiya 16 daga Arewacin Najeriya sakamakon zargi maras tushe da aka yi musu a jihar Edo.

An ce ƴan sa-kai sun zarge su da garkuwa da mutane, lamarin da ya haddasa kashe su ba tare da wani bata lokaci ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng