Fadar Sarkin Musulmi Ta Faɗi Dalilin da Ya Sa Take Amfani da Ganin Watan Saudiyya a Najeriya

Fadar Sarkin Musulmi Ta Faɗi Dalilin da Ya Sa Take Amfani da Ganin Watan Saudiyya a Najeriya

  • Kwamitin ganin wata na faɗar sarkin Musulmi ya yi bayanin yadda ake tantance ganin wata ko da ilimi ya nuna ba za a gan shi ba a Najeriya
  • Malam Simwal Usman ya sake nanatawa cewa a ilimin falaki dai ba za a ga watan sallah ranar Asabar watau 29 ga watan Ramadan ba
  • Amma ya ce idan an gan shi a kasashe kamar Saudiyya, kwamitin fatawa na fadar sarkin kan ba da fatawar za a iya amfani da ganinsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Ɗaya daga cikin ƴan kwamitin ganin wata na fadar sarkin Musulmi, Simwal Usman Jibrin ya bayyana yadda ake duban wata da tantancewa kafin a sanar a Najeriya.

Masanin ilimin taurarin ya ce idan kwamitin ganin wata ya tattara rahotannin da ya samu, ya na miƙawa sarkin musulmi ne domin yanke hukuncin ƙarshe.

Kara karanta wannan

Azumi 30: Abin da ya sa ba zai yiwu a ga jinjirin watan Shawwal a ranar Asabar ba

Simwal Usman da sultan.
Yadda sarkin musulmi ke ɗaukar ganin watan Saudiyya a wasu lokutan Hoto: Simwal Usman, Daular Usmaniyya
Asali: Facebook

Malam Simwal ya yi wannan bayani a wata hira da DCL Hausa ta yi da shi kan yiwuwar ganin jinjirin watan Shawwal ranar Asabar, 29 ga watan Ramadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a ga wata ranar Asabar a Najeriya?

Simwal ya bayyana cewa a bincikensu na masana, sun tabbatar da cewa ba za a ga wata ranar Asabar ba.

A cewarsa, za a samar da watan ne da misalin karfe 11:58 na safiya a ranar Asabar, wanda ke nuna zuwa faɗuwar rana watan ba zai wuce awanni 6 da mintuna 40 ba.

Ya jaddada cewa a ilimin falaki, ba za a iya ganin watan da bai wuce awanni 6 da minti 40 ba da ƙwayar ido, don haka a ganinsu ba za a ga wata ba ranar Asabar.

Simwal ya ƙara da cewa ko da ilimi ya nuna ba za a ga wata ba, za a iya samun waɗanda za su ce sun ga wata ko kuma ƙasashen gabas kamar Saudiyya su gani.

Kara karanta wannan

Yadda Musulmi zai yi bikin sallah da Idi cikin nishadi a tsarin Musulunci

Sarkin musulmi na ɗaukar ganin watan Saudiyya?

Ya ce idan irin haka ta faru, kwamiti kan miƙa rahoto ga sarkin Musulmi shi kuma ya nemi shawara daga kwamitin fatawa karkashin jagorancin Sheikh Sharif Saleh.

"A a gaskiya a ilimance ba za a gan shi ba, amma ire-iren wannan ta faru kuma za ka ji wasu sun ce sun ganshi ko ƙasashen gabas su ce sun ganshi.
"Abin da Mai alfarma sarkin musulmi yake yi shi ne ya tuntuɓi kwamitin fatawa karkashin jagorancin Sheikh Sharif Saleh, su ake ba damar yin fatawa shin za a amshi ganin nan ko kuwa."
"Wani lokacin suna ba da fatawar cewa tun da ƙasashen gabas sun gan shi kamar Saudiyya, magabata sun ce idan ƙasashen da ke gabas da ku sun gan shi to za ku iya amfani da shi.

- In ji Simwal.

Simwal Usman.
Wasu lokutan ana ba Sarkin Musulmi fatawar bin Saudiyya wajen ganin wata Hoto: Simwal Usman Jibril
Asali: Twitter

Sarkin Musulmi ke yanke shawara ta karshe

Masanin ya tabbatar da cewa sarkin Musulmi ke yanke shawara da kwamitin fatawa kan amsar ganin wata duk da ilimin falaki ya ce ba za a ganshi ba.

Kara karanta wannan

Kasar Saudiyya ta fitar da sanarwa kan duba watan sallar azumi

Ya musanta zargin cewa kwamitin ganin wata na bin duk abin da Saudiyya ta sanar, ya na mai cewa a ilimi, duk watan da aka gani a can za a iya ganinsa a Najeriya.

"Watan nan guda ɗaya ne kuma banbancin lokacinmu da Saudiyya awa biyu ne kacal, don haka har in za a iya ganin wata a Saudiyya to za a ganshi a Najeriya."

Yaushe za a yi sallah a Saudiyya?

A wani labarin, kun ji cewa ƙasashen gabas kamar Saudiyya da Qatar sun fara shirin fita duban watan karamar sallah ranar Asabar, 29 ga watan Ramadan.

Hasashen ya bayyana ranakun da ake kyautata zaton waɗannan ƙasashe za su yi sallah a bana bayan kammala azumi 29 ko 30.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262