Bayan Janye Hawan Sallah, an Karrama Aminu Ado da Lambar Yabon Zaman Lafiya
- Ƙungiyar Nigerian Citizens Peace Ambassadors ta karrama Mai Martaba Aminu Ado Bayero da lambar yabo kan zaman lafiya
- Rahotanni sun tabbatar da cewa karramawar ta zo ne kwanaki bayan ya janye daga hawan sallah don guje wa rikici a jihar Kano
- Tun bayan sauke shi daga sarauta da gwamnatin Kano ta yi a 2024, rikicin masarautar Kano ya ci gaba da daukar salo iri-iri
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya karɓi baƙuncin ƙungiyar Nigerian Citizens Peace Ambassadors a fadarsa da ke kofar Nasarawa.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Yahaya Imam Sulaiman, ne ya jagoranci tawagar da ta miƙa masa lambar yabo kan zaman lafiya a Najeriya.

Asali: Twitter
Legit ta gano yadda aka karrama mai martaba Aminu Ado Bayero ne a cikin wani sako da shafin masarautar Kano ya wallafa a X a ranar Jumu'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan Aminu Ado Bayero ya janye daga gudanar da hawan sallah domin gujewa rikici da tashin hankali a fadin jihar Kano.
An karrama Aminu Ado kan zaman lafiya
A yayin wata ziyara, ƙungiyar Nigerian Citizens Peace Ambassadors ta karrama Alhaji Aminu Ado Bayero da lambar yabo kan zaman lafiya.
Kungiyar ta bayyana cewa lambar yabon da ta ba Aminu Ado Bayero na nuni da irin rawar da ya taka wajen tabbatar da zaman lafiya a Kano.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Yahaya Imam Sulaiman ne ya jagoranci tawaga domin karrama Aminu Ado Bayero saboda yadda yake ba da gudunmawa wajen wanzar da zaman lafiya.
Wannan karramawa ta biyo bayan matakin da Aminu Ado Bayero ya dauka na kin yin hawan sallah domin gujewa rikici a Kano.
A halin yanzu dai, bangaren Muhammadu Sanusi II ne zai jagoranci hawan sallah a jihar bayan matakin da bangaren Aminu Ado Bayero ya dauka.
Kano: Rikicin Aminu da Sanusi na ci gaba
Tun bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke Aminu Ado Bayero tare da mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki, rikicin masarauta ya dauki sabon salo.
Masu goyon bayan Aminu Ado Bayero na ganin cewa sauke shi daga karagar mulki ba bisa doka ba ne, yayin da magoya bayan Muhammadu Sanusi II ke cewa an yi adalci.

Asali: UGC
Lambar yabon za ta yi tasiri a rikicin Kano?
A yanzu dai ba a san ko lambar yabo da aka bai wa Aminu Ado Bayero za ta sanya shi ya hakura da sarautar Kano ba.
Duk da haka, ana ci gaba da sanya idanu kan yadda rikicin zai kaya, musamman bayan hawan sallah da bangaren Muhammadu Sanusi zai jagoranta.
Sanusi II ya ziyarci Abba Kabir Yusuf
A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara wa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnati.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Muhammadu Sanusi II ya samu rakiyar wasu jiga jigan fadar Kano da suka hada da Sarkin Yaki da Wamban Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng