An Hallaka Kachalla Dan Isuhu da Ya sa Haraji a Kauyuka 21 Ya Kashe Farfesa Yusuf
- Rahotanni na nuni da cewa jami’an tsaro sun yi nasarar hallaka fitaccen ɗan ta’adda Ɗan-Isuhu wanda ya addabi al’ummar Zamfara da Katsina
- An tabbatar da mutuwar Dan-Isuhu, wanda yake dan uwa ga Ado Aleru, bayan wata fafatawa mai zafi da jami’an tsaro suka yi da shi
- Rahotanni sun tabbatar da cewa Ɗan-Isuhu ya kasance sanannen jagoran ayyukan ta’addanci da suka hada da kisan jami’an tsaro da satar mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Rahotanni da suka fito daga jihar Zamfara na nuni da cewa jami'an tsaro sun samu nasarar kashe dan ta'adda, Kachalla Ɗan-Isuhu.
Ta’addancin Ɗan-Isuhu ya jefa jama’a cikin firgici tsawon shekaru, musamman a yankunan Tsafe, Ɗansadau, da wasu sassan Katsina.

Asali: Facebook
Hadimin shugaba Bola Tinubu, Abdulaziz Abdulaziz ne ya sanar da cewa dakarun Najeriya sun kashe shi a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan-Isuhu ya kasance yana kai hare-hare a kan jami’an tsaro da fararen hula, inda ya shahara wajen garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.
Wata majiya daga jami’an tsaro ta tabbatar da cewa an kashe Ɗan-Isuhu ne bayan wata fafatawa mai zafi da suka yi da shi a Keta, Zamfara.
Ɗan-Isuhu: Ɗan ta’addan da ya addabi Zamfara
Ɗan-Isuhu ya fara samun ƙaurin suna tun a shekarar 2019, inda ya jagoranci kai hare-hare a yankunan Tsafe, Ɗansadau, da yankunan Katsina.
Abubakar Bala Ibrahim Tsahe ya wallafa a Facebook cewa shi ne ya kitsa kisan jami’an soji biyar a Wanzamai, ya sace ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Gusau da 'yan NYSC a hanyar Kucheri-Tsafe.
A bara, ya jagoranci harin da aka kai a garin Tsafe inda aka kashe Shugaban Askawara tare da yin garkuwa da ma’aikatan kamfanin Setraco 14.
Wasu laifuffukan Kachalla Ɗan-Isuhu
Baya ga hare-haren da ya kai a Zamfara da Katsina, Ɗan-Isuhu ya kashe jami’an CTU huɗu da ke aiki a kamfanin Setraco a Tabanni.
Ya kuma kashe mutum 21 a Bilbis a shekarar da ta gabata tare da karɓar kuɗin fansa na sama da miliyan 200 daga garuruwa 21 a karamar hukumar Tsafe.
Ya hallaka ‘yan sanda biyu da ke tsaron Kwalejin Kiwon Lafiya da Fasaha ta Tsafe da kuma kashe Askarawa tara a Gidan Kaji, Tsafe.
Haka zalika ana zargin cewa shi ne ya jagorance kashe Farfesa Yusuf Sa'idu na jami'ar Usman Danfodiyo a bara.

Asali: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa Dan Isuhu ya yi alkawarin kashe akalla mutum daya a duk wunin da aka yi na Ramadan.

Kara karanta wannan
'Dan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu ya gamu da fushin matasa, an dakawa motar tallafinsa wawa
An ruwaito cewa dan ta'addan ya tattara kudin fansa a kauyuka da dama da suka kai Naira miliyan 800.
Yadda aka kashe Ɗan-Isuhu
Ɗan-Isuhu ya kasance barazana har ga ‘yan ta’adda irinsa, inda ya rinjayi da dama daga cikinsu yayin fada da juna.
Gwamnati ta rufe hanyar Funtua-Yankara-Wanzamai-Tsafe-Gusau daga ƙarfe 6:30pm zuwa 6:00am na tsawon shekara guda saboda ta’addancinsa.
A ƙarshe, Ɗan-Isuhu ya gamu da ajalinsa yayin da aka yi masa kwanton ɓauna a tsakanin Keta da Danjiba, bayan fafatawa da jami’an tsaro a Keta da ta yi sanadin mutuwar mayakansa da dama.
Lakurawa sun kai hari a Kebbi
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan ta'addan Lakurawa sun kai wani mummunan hari jihar Kebbi da ke Arewa ta Yamma.
Rahoton Legit ya tabbatar da cewa 'yan ta'addar sun samu nasarar hallaka mutane yayin da suka kai farmakin kan jama'ar da basu ji ba, ba su gani ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng