Jerin Kura Kurai 5 da Musulmi Ke Yi a Ranar Ƙaramar Sallah da Yadda Za a Kauce Masu

Jerin Kura Kurai 5 da Musulmi Ke Yi a Ranar Ƙaramar Sallah da Yadda Za a Kauce Masu

Ƙaramar sallah tana ɗaya daga cikin idi guda biyuda musulmi a ko'ina a faɗin duniya suke yi a kowace shekara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

A lokacin shagulgulan sallah, al'ummar musulmi su na farin ciki da godiya ga Allah S.W.T bayan kammala ibadar azumin watan Ramadan.

Sallah.
Abubuwan da ya kamata musulmi ya guje wa a ranar sallah Hoto: Getty Images
Asali: Facebook

A wannan shekara 2025, ana sa ran za a yi idin ƙaramar sallah ne ranar Lahadi, 30 ga watan Maris, ko kuma ranar Litunin, 31 ga watan Maris, 2025, ruwayar Punch.

Tuni dai al'ummar musulmi a Najeriya da sauran ƙasashen duniya suka fara shirin sallah yayin da azumi ya fara bankwana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma saboda murna ko wani abu makamancin haka, wasu mutane suna aikata kura-kurai da ka iya rage albarka da ladansu a wannan rana ta Eid-ul-fitr.

Duk da ba za a ce mutum ya aikata haramun ba, amma waɗannan kura-kurai abubuwa ne da ya kamata a guje masu.

Kara karanta wannan

Masu bautar kasa a Najeriya na cikin alheri dumu dumu, Tinubu ya fara biyan N77, 000

Legit Hausa ta tattaro maku wasu daga cikin waɗannan kura-kurai da yadda ya kamata musulmi ya kauce masu. Ga su kamar haka:

1. Jinkiri ko rasa sallar idi

Sallar Idi wajibi ce ga duk wanda ya sami damar halarta, amma wasu sukan makara ko kuma su shagaltu da shiri har su rasa ta.

An ruwaito cewa Annabi (SAW) da sahabbansa su kan yi duk mai yiwuwa wajen halartar Sallar Idi a jam’i (Sahih Bukhari).

Bisa haka, ya kamata mutane su riƙa kokarin shiryawa da wuri, su yi wankan idi da sauran sunnonin da suka tabbata daga Manzon Allah, sannan a tafi masallacin idi akan lokaci.

2. Rashin ba da zakkar fidda kai kafin sallar Idi

Zakkatul Fitr ko a ce zakkar fidda kai wajibi ce ga kowane Musulmi mai hali, kuma yana da kyau a bayar da ita kafin a tafi filin idi.

Fitar da wannan zakka ƙafin ranar sallah yana da matuƙar muhimmanci domin zai ba talakawan da ba su da hali damar yin shagalin sallah cikin farin ciki.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Dalung ya yi gargadi kan 'shirin' saka dokar ta baci a Kano

Wasu malamai magabata kamar Ibn Majah na ganin bayar da zakkar bayan an sauko sallar idi kurkure ne da ke maida ita sadaƙa.

Malamai sun shawarci musulmai masu hali da su yi ƙoƙarin ba da zakkar kafin a tafi sallah domin samun lada cikakke.

3. Rashin yin kabbarbari bayan ganin wata

Rahoton The Muslim Vibe ya nuna cewa ana so musulmi ya yi kabbarbarin godiya ga Allah bisa kammala azumin Ramadan.

Ana fara yi ne da zaran an tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal har zuwa washegarin ranar sallah.

Masallacin idi.
Kura kuran da mutane ke aikatawa a ranar sallah karama da hanyar guje masu Hoto: Idris Ahmad
Asali: Twitter

Malam Auwal Isma'il ya shaida mana cewa waɗannan kabbarbari suna da matuƙar muhimmanci, ba a son musulmi ya yi wasa da su.

Ya ce:

"Ina ba mutane shawara kada su yi wasa da kabbarbarin nan, godiya ce ga Allah na gama azumi lafiya, mutum nawa ne aka fara amma ba a gama da su ba?"
"Kabbarbarin su ne, Allahu Akbar, Allahu Akbar, La'ilaha ilaLlah, Allahu Akbar, Allahu Akbar Wa Lillahil Hamd."

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta yi magana kan shirin hawan sarakuna 2 a Kano

A cewar malamin, rashin yin waɗannan kabbarbari ba karamin kuskure ba ne, ya kamata "mu rika tunatar da juna don kada mu yi wasa da su,"

4. Komawa aikata zunubi bayan azumi

Ranar Sallah rana ce ta ibada, godiya da farin ciki, amma wasu mutane suna amfani da ita wajen yin abubuwan da suka sabawa addini.

Wasu na amfanin da wannan rana wajen kauce hanya kamar sauraron kiɗan banza, haɗuwa da mata da maza ba bisa ka’ida ba, ko kuma ɓarnatar da dukiya.

Annabi (SAW) ya ce, "Mafi alherin mutane su ne masu tsoron Allah a cikin farin ciki da bakin ciki." (Tirmidhi).

Sallah.
An hana musulmi yin azumi ranar sallah Hoto: Getty Images
Asali: Twitter

Wannan ya sa malamai ke jan hankalin musulmai su guji shirya tarukan da suka saɓawa shari'ar musulunci kuma da sunan murnar zuwan sallah.

A baya bayan nan, Mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya buƙaci jama'a su riƙe kansu, ka da su koma aikata laifukan da suka bari da azumi.

Kara karanta wannan

Ramadan: Dan Majalisa Kirista ya yi wa Musulmi bazata bayan bukatar babban limami

Sultan ya ce ana son musulmai su ci gaba da aikata ayyukan alheri tare da nisantar saɓo har bayan watan azumi.

5. Azumi ranar sallah

Shari'ar addinin musulunci ta haramta yin azumi a kowace ɗaya daga cikin idi biyu da muke da su, ƙaramar sallah da babbar sallah.

Bisa kuskure ko rashin sani, ana samun wasu su tashi da azumin nafila, ramuwa ko wani abu mai kama da haka, rahoton Islamqa

Haramun ne yin azumin ranar idi saboda hadisin Abu Sa’eed al-Khudri (Allah Ya ƙara yarda da shi) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya hana yin azumin ranar idin ƙaramar sallah ko babba.  (Muslim ya ruwaito, 827).

Alamun daren Lailatul Qadr

A baya kun ji muhimman alamun da ake gane daren Lailaful Qadr da su a goman ƙarshe na watan azumin Ramadan.

Manzon Allah (S.A.W) ya kwaɗaitar da neman daren Lailatul Qadari a ranakun mara watau 21 23, 25, 27 da 29 ga Ramadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262