Tsohon Hadimin Matawalle Ya Tabo Batun Dokar Ta Baci a Zamfara, Ya ba Tinubu Shawara

Tsohon Hadimin Matawalle Ya Tabo Batun Dokar Ta Baci a Zamfara, Ya ba Tinubu Shawara

  • Tsohon hadimin Bello Matawalle da ya ke gwamna, ya yi fatali da kiran da wasu ke yi na a sanya dokar ta ɓaci a jihar Zamfara
  • Sani Abdullahi Shinkafi ya bayyana cewa masu kiran a sanya dokar ta ɓaci maƙiyan Zamfara ne kuma ya kamata a bincike su
  • Ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi da kiran da aka yi masa na sanya ɗokar ta ɓaci kamar yadda aka yi a Ribas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Tsohon mai ba tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, shawara na musamman, Sani Abdullahi Shinkafi, ya yi magana kan kiran a sanya dokar ta ɓaci a Zamfara.

Sani Abdullahi Shinkafi ya yi watsi da kiran da wasu suka fara yi na a ayyana dokar ta ɓaci a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Gwamnan Nasarawa ya zabi wanda zai gaje shi? Ya fadi gaskiya

Ana so a sanya dokar ta baci a Zamfara
Sani Abdullahi Shinkafi ya yi fatali da batun sanya dokar ta baci a Zamfara Hoto: Sani Abdullahi Shinkafi, Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Tsohon hadimin na Matawalle ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sani Abdullahi Shinkafi ya jaddada cewa sauke gwamna, mataimakinsa da ƴan majalisar dokokin jiha abu ne da ya saɓawa doka da kundin tsarin mulki.

Wace shawara aka ba Bola Tinubu?

Ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya yi watsi da wannan kira, wanda a cewarsa yana fitowa ne daga ƴan siyasan da suka gaza, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

Tsohon ɗan takarar gwamnan ya kuma buƙaci Gwamna Dauda Lawal da ya ci gaba da mayar da hankali wajen kawo ci gaba da kyautata rayuwar al’ummar jihar.

"Waɗanda ke kira da a ayyana dokar ta-baci a cikin yanayi na zaman lafiya, haɗin kai, kwanciyar hankali, tsaro, da ci gaban tattalin arziki a jihar Zamfara abokan gaba ne ga al’ummar jihar."
"Ba kawai kamata ya yi a yi banza da su ba, ya dace jami’an tsaro su bincike su don gano manufarsu da kuma masu ɗaukar nauyinsu."

Kara karanta wannan

Sanatan Bauchi ya ba mutane kunya da azumi, bidiyosa yana rabon kuɗi ya shiga intanet

“Abin takaici ne yadda wasu ƴan siyasa da ta ƙare musu ke ɗaukar nauyin matasa da wasu ƙungiyoyi don su nemi a ayyana dokar ta ɓaci a jihar Zamfara, yayin da tsaro da zaman lafiya suka inganta matuƙa."
"Ingantar tsaro ya ba da damar haɓakar tattalin arziki da ci gaban ababen more rayuwa da suka gagara shigowa jihar tsawon shekaru 13 saboda matsalar ƴan bindiga tun kafin Gwamna Dauda Lawal ya hau mulki a 2023."
“Muna yabawa Shugaba Tinubu da rundunar soji bisa ci gaba da fatattakar ƴan bindiga da sauran ɓata-gari a jihar Zamfara da yankin Arewa maso Yamma baki daya."
“Wannan ya yi daidai da tanadin sashe na 14(2)(b) na kundin tsarin mulkin 1999 (da aka yi wa gyara), wanda ke cewa tsaro da jin daɗin al’umma su ne ginshikan aikin gwamnati."

- Sani Abdullahi Shinkafi

Bola Tinubu ya ba ƴan APC shinkafa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya raba kyautar shinkafa ga mambobin jam'iyyar APC a jihar Zamfara.

Shugaba Bola Tinubu ya raba buhunan shinkafa 7,000 ga ƴaƴan jam'iyyar APC a matsayin kyautar watan azumin watan Ramadan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel