Surukar Ganduje kuma Hadimar Ministan Tinubu Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Surukar Ganduje kuma Hadimar Ministan Tinubu Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

  • 'Diyar tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Sanata Abiola Ajimobi ta riga mu gidan gaskiya tana da shekaru 42 a duniya
  • Marigayiya Bisola Kola-Daisi ita ce yar fari ga tsohon gwamna na Oyo wanda ta rasu a birnin Landan da ke kasar Birtaniya
  • Kafin rasuwarta ta kasance shugabar kamfanin Grandex Nigeria Ltd. kuma ta kafa katafaren shagon kaya na Florence H. Luxury
  • Har ila yau, Bisola ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara ta musamman ga Ministan Kasafi da Tsare-tsare, Atiku Bagudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Iyalan tsohon gwamnan Oyo, marigayi Sanata Abiola Ajimobi sun yi babban rashi.

Bisola Kola-Daisi, ‘yar fari ga tsohon gwamnan ta rasu a birnin Landan tana da shekaru 42 a duniya.

Diyar tsohon gwamna ta riga mu gidan gaskiya
Babbar ƴar tsohon gwamnan Oyo, marigayi Abiola Ajimobi ta rasu. Hoto: @poweronline365.
Asali: Twitter

Wanene marigayi Abiola Ajimobi a Najeriya?

Kara karanta wannan

Siyasa kenan: Bayan kare El Rufai a baya, shugabar matan APC ta dawo caccakarsa

TheCable ta bayyana cewa kafin rasuwar Bisola, ta rike muƙamin mai ba ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu, shawara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayiyar wacce ɗiya ce ga marigayi Abiola Ajimobi wanda aka haife shi a ranar 16 Disamba 1949 wanda ya rasu a ranar 25 Yuni 2020.

Dan siyasar ya rike muƙamin gwamnan Jihar Oyo daga shekarar 2011 zuwa 2019, shi ne mutum na farko da aka zaɓa sau biyu a wannan muƙami.

A shekarar 2003, Abiola Adeyemi Ajimobi ya zama Sanata a majalisar Tarayyar Najeriya, cewar shafin Wikipedia.

Ya riƙe muƙamin jami’i mai muhimmanci a Majalisar Dattawa, inda ya zama Mataimakin Shugaban ’Yan Adawa.

A 2007, Ajimobi ya tsaya takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar ANPP amma bai ci ba, a 2011, ya sake tsayawa takara ƙarƙashin jam’iyyar ACN inda ya yi nasara.

'Yar marigayi tsohon gwamnan Oyo ta rasu
An sanar da rasuwar babbar ƴar tsohon gwamnan Oyo, marigayi Abiola Ajimobi. Hoto: @abi_kd.
Asali: Instagram

Ƴar tsohon gwamna ta riga mu gidan gaskiya

Marigayiyar, wacce take ‘yar fari ga Ajimobi, matar sanannen ɗan siyasa da jami’in banki, Kolapo Kola-Daisi ce, kuma mahaifiyar yara guda uku.

Kara karanta wannan

An shiga jimami a Kano: Babban mai taimaka wa Gwamna Abba ya rasu ana azumi

Mijinta, Kolapo, ya bayyana damuwarsa a shafinsa na sada zumunta, yana cewa:

“Duniya ta rasa tauraruwa mai haske, Bisola ba matata kawai ba ce; abokiyata ce a komai, ruhinta zai rayu a cikin ‘ya’yanmu.”

Bisola, mai taimakon jama’a, ta yi suna sosai a harkar kasuwanci inda ta mallaki kamfanoni.

Ita ce shugabar kamfanin Grandex Nigeria Ltd., babbar cibiyar sayar da kayayyaki da aka kafa a 1984, kuma ta kafa shagon kaya na Florence H. Luxury.

Kafin rasuwarta, Bisola ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara ta musamman ga Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Atiku Bagudu.

Iyalan Kola-Daisi da Ajimobi ba su fitar da wata sanarwa kan rasuwarta ba a hukumance.

An sanar da rasuwar hadimin Abba Kabir

Kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta yi jimami bayan sanar da rasuwar Abdullahi Tanka Galadanci, babban mai taimakawa Abba Kabir Yusuf kan Rediyo.

Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa Galadanci ya rasu bayan gajeruwar jinya a asibiti.

Gwamnan Kano ya bayyana marigayin a matsayin ginshiki a gwamnatinsa, ya na mai addu’ar Allah ya gafarta masa, ya kuma ba iyalansa hakuri.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng