'Aminu Ado Ka Hakura da Mulkin Kano,' Kiran Jama'a bayan Janye Hawan Sallah
- Mutane sun fara magana bayan mai martaba Aminu Ado Bayero ya janye shirin hawan Sallah don tabbatar da zaman lafiya a Kano
- Ana ganin wannan mataki ya ba da damar Sarki Muhammadu Sanusi II ya jagoranci hawan Sallah cikin kwanciyar hankali
- Jama'a sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan, wasu na yaba masa yayin da wasu ke kira da ya hakura da mulkin baki daya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Biyo bayan fargabar samun rikici sakamakon shirin hawan Sallah tsakanin bangaren Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II, an samu kwanciyar hankali.
Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa ya yanke shawarin dakatar da hawan sallah ne domin tabbatar da zaman lafiya da kuma kiran da da aka masa.

Asali: Twitter
A daren Laraba ne mai martaba Aminu Ado Bayero ya yi bayanin dakatar da hawan sallah a wani bidiyo da aka wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yanzu haka, ana sa ran Muhammadu Sanusi II zai jagoranci hawan Sallah a Kano ba tare da wata matsala ba.
Martanin jama'a kan matakin Aminu Ado
Matakin janyewar Aminu Ado Bayero daga hawan Sallah ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka bayyana ra’ayoyinsu.
Bilyameen Abdullahi Snk ya jinjinawa Aminu Ado Bayero, ya na mai cewa:
"Duk da cewa na fi goyon bayan Sarki Sanusi II, amma gaskiya ka burge ni da dattako da sanin yakamata.
Ka tabbatar da zaman lafiya a Kano da al’ummarta baki daya. Allah ya ja kwana kuma ya kawo babban rabo mai albarka."
Usman Farouk Tijjani kuwa ya nuna shakku, inda ya ce:

Kara karanta wannan
Abin da Shehu Sani ya ce bayan Aminu Ado ya janye hawan sallah, ya shawarci Sanusi II
"Ta ya ya za ka yi hawan Sallah alhali ba ka da hakimi ko daya?"
Habu Atafi’n Hadejia ya yaba da matakin Aminu Ado, ya na cewa:
"Aminu ba ya fada kuma ba ya son fada. Wannan ne lakabinka kuma yau ka tabbatar wa da duniya haka ne.
"Allah ya saka da alheri bisa wannan hukunci da ka yanke don zaman lafiyar Kano."
Wasu mutane kuwa sun bayyana fushinsu kan yadda rikicin masarautar ke shirin wargaza jihar Kano.
Mustapha Tasleem ya ce:
"Ba na goyon bayanka saboda matsin lambar gwamnatin tarayya. Amma ka tabbatar wa duniya cewa har yanzu ka na kan turban mahaifinka, marigayi Alhaji Ado Bayero.
"Allah ya ji kansa da rahama ya kuma zaunar da kasa lafiya baki daya."
Idris Garba ya yi tsokaci da cewa:
"Da haka yayi tun farko da ya fi kima da daraja a gaban al’umma,"

Kara karanta wannan
"Sun haƙura?" An saki bidiyon Sanusi II bayan Aminu Ado ya janye hawan sallah a Kano
Dawaki Baffa ya soki masarauta, yana mai cewa:
"Kun ji kunya da kuka ba da kafa har yara marasa tarbiyya suna iya fadan maganganu marasa dadi a kanku.
"Ku sani, ba irin rikon da ku ka yi wa gadon masarauta aka yi masa ba, da ba ku samu sarauta ba."

Asali: Facebook
Kiran Aminu Ado ya hakura da mulki
Wani mazaunin Kano a unguwar 'Yan Kaba, Musa Adamu ya bayyana wa Legit cewa ya ji dadin matakin da mai martaba Aminu Ado ya dauka.
Musa Adamu ya ce:
"Lallai abin farin ciki ne. Ina ma a ce zai hakura da batun sarautar baki daya kowa ya huta.
"Ba wai ana goyon bayan Sanusi ba ne, yadda aka sauke Sanusi shi ma haka aka sauke shi. Da hakura ya yi, da ya fi."
Har yanzu, ana ci gaba da musayar yawu tare da bayyana ra'ayoyi kan janyewar da Aminu Ado ya yi musamman a kafafen sada zumunta na X da Facebook.

Kara karanta wannan
Sheikh Lawan Triumph ya sa baki kan rikicin hawan sallah a Kano, ya aika sako ga Aminu Ado
Ya zama ruwan dare 'yan Najeriya su taso lamari irin wannan a gaba don tofa albarkacin bakinsu tare da tsokaci kan wadanda suke goyon baya.
Lamarin sarautar Kano ya zama babban abin maida hankali a Arewacin Najeriya, inda ake daura laifin rigimar masarautar kan gwamnonin jihar na yanzu da wadanda suka shude.
Hakimin Bichi ya ziyarci Sanusi II
A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin sarauta da na addini daga karamar hukumar Bichi sun ziyarci Muhammadu Sanusi II.
A cikin tawagar da ta kai ziyarar akwai shugaban karamar hukumar Bichi, Hakimin Bichi, dagatai, masu unguwanni, limamai da sauransu.
Salisu Ibrahim ya fadada wannan labarin ta hanyar bayyana karin bayani a kan rigimar masarautar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng