'Yan Ta'addan Lakurawa Sun Kai Farmaki a Kebbi, Sun Hallaka Jami'an Tsaro
- Ƴan ta'addan ƙungiyar Lakurawa da ake zargin sun fito daga kasashen waje sun farmaki jami'an tsaro na hukumar Kwastam a jihar Kebbi
- Sun hallaka jami'an Kwastam mutum biyu tare da wani mutum ɗaya a harin da suka kai a ƙauyen Bachaka na ƙaramar hukumar Argungu
- Rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce harin ba zai karya gwiwar jami'an tsaro wajen fatattakar ƴan ta'adda ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Ƴan ta'addan Lakurawa sun kai hari kan jami'an tsaro na hukumar Kwastam a jihar Kebbi.
Ƴan ta'addan sun hallaka jami'an Kwastam mutum biyu tare da wani mutum ɗaya, a harin da suka kai a ƙauyen Bachaka da ke ƙaramar hukumar Argungu.

Asali: Original
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan ta'addan sun kai harin ne a ranar Talata, 25 ga watan Maris 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin dai na zuwa ne bayan sa’o’i 24 kacal da haɗakar jami’an tsaro suka kashe wasu ƴan ta'addan ƙungiyar Lakurawa guda biyu a yankin.
Ƴan sanda sun tabbatar da harin Lakurawa
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sanda jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, ya ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku, ciki har da jami’an Kwastam biyu da wani mazaunin yankin.
"Eh, lallai an kai hari a yankin, kuma sakamakon hakan, an kashe jami’an Kwastam guda biyu da wani mazaunin garin Bachaka."
- DSP Nafiu Abubakar
DSP Nafiu Abubakar ya bayyana cewa tuni kwamishinan ƴan sanda na jihar, CP Sani Bello, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru domin duba halin da ake ciki da kuma ƙarfafawa jami’an tsaro gwiwa.
A nasa martanin, kwamishinan ƴan sanda, CP Sani Bello, ya jaddada cewa jami’an tsaro ba za su bari irin waɗannan hare-hare su razana su ba, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Kara karanta wannan
Katsina: 'Yan sanda sun dakile mugun nufin 'yan bindiga, sun kubutar da bayin Allah
Ya ce rundunarsu za ta ci gaba da fatattakar ƴan ta’addan har sai an kawar da su gaba ɗaya daga yankin.

Asali: Twitter
A cewarsa, irin waɗannan hare-hare na nuna cewa ƙungiyar Lakurawa ta rage ƙarfi sakamakon ci gaba da matsin lamba da jami’an tsaro ke yi musu.
"Mun fahimci cewa waɗannan hare-hare alamu ne da ke nuna cewa sun fara karaya sakamakon ci gaba da kai musu farmaki da ake yi."
"Jami’an tsaro za su ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace don tabbatar da cewa an gama da su gaba ɗaya."
- CP Sani Bello
Ƴan ta'adda sun farmaki sansanonin sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'addan Boko Haram ɗauke da makamai sun kai farmaki kan sansanonin sojoji biyu a jihar Kebbi.
Ƴan ta'addan sun farmaki sansanonin sojojin ne a ƙananan hukumomin Damboa da Gambarou Ngala na jihar.
A yayin farmakin an hallaka jami'an sojoji biyu yayin da aka kashe ƴan ta'addan na Boko Haram masu tarin yawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng