"Ba Abin a Mutu ko a Yi Rai ba ne," Aminu Ado Ya Canza Shawarar Hawan Sallah a Kano
- Yayin da mazauna Kano ke cikin fargabar abin da zai faru a bukukuwan hawan Sallah, Aminu Ado Bayero ya fitar da matsaya
- Ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan shawarwari daga malamai, iyaye, shugabanni, da masu ruwa da tsaki a masarauta
- Ya bukaci jama’a da su yi hakuri da wannan mataki tare da amfani da bukukuwan Sallah wajen sada zumunci da ƴan uwa a Kano
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kawo karshen fargabar da wasu mazauna jihar suka shiga kan batun hawan Sallah guda biyu.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa an dakatar da dukkan shirye-shiryen da fadarsa ta yi na gudanar da hawan bukukuwan Karamar Sallah a jihar.

Kara karanta wannan
"Sun haƙura?" An saki bidiyon Sanusi II bayan Aminu Ado ya janye hawan sallah a Kano

Asali: Facebook
A cikin bidiyon da aka wallafa a shafin Facebook na masarautar, Sarkin Kano na 15 ya bayyana dalilan da suka sa ya janye shirin gudanar da hawan..
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin Ado Bayero na janye hawan sallah a Kano
Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da cewa an dakatar da hawan Sallah ne domin ceton rayukan jama’a da tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce:
"Mu na sanar da dukkan jama'armu, kuma muna hakurtar da su, kan wannan hukunci da mu ka yi na janye haye-hayen Salla,saboda kiyaye zaman lafiya a garinmu mai albarka, Kano da kasa baki daya."
Alhaji Aminu Ado Bayero ya kara da cewa hawan Sallah ba abu ne na a mutu ko a yi rai ba, saboda haka, ba zai zura ido rayuwar jama'ar da ya yi rantsuwar kare wa ta salwanta ba.
Hawan Sallah: Ado Bayero ya gana da manya

Kara karanta wannan
Sheikh Lawan Triumph ya sa baki kan rikicin hawan sallah a Kano, ya aika sako ga Aminu Ado
Ya ƙara da bayyana cewa ba gaba-gaɗi aka ya ke hukuncin dakatar da hawan Sallar da ya shirya gudanar wa ba, sai da aka gana da masu ruwa da tsaki.

Asali: Facebook
Ya ce:
"Yanke wannan hukunci, ya biyo bayan nasihohi da mu ka samu daga malumanmu da muke ganin girmansu da darajar su.
@Sannan da kiraye-kiraye daga iyaye da shugabanni, wadanda suka isa da mu, sannan da kuma shawara da muka yi da ƴan majalisarmu."
Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce, a matsayinsa na 'Sarkin Kano,' ya dauki alkawarin kiyaye imani, mutunci, dukiya, da zaman lafiyar al’umma.
Wannan ne ya sa ya ga dacewar daukar wannan mataki domin kaucewa duk wani abu da ka iya haddasa tashin hankali.
Aminu Ado Bayero ya ba masoyansa hakuri
Mai Martaba Aminu Ado Bayero ya bukaci al’umma da sauran masoya su yi hakuri da wannan hukunci da aka zartar domin dorewar zaman lafiya a jihar Kano da kuma kasa baki ɗaya. Ya yi amfani da damar wajen kira ga al’umma da su yi amfani da lokutan bukukuwan Sallah wajen ziyartar juna domin sada zumunci.
Aminu Ado Bayero, ya kuma taya al’ummar musulmi addu’ar samun dacewar Ubangiji daga cikin bayinsa waɗanda Allah yake gafartawa da yin rahama tare da karɓar ibadar da aka gudanar.
Yan sandan Kano sun magantu kan hawan Sallah
A baya, mun wallafa cewa rundunar ‘yan sanda ta bukaci mutane da su yi kula da kyau don gujewa duk wani tashin hankali da ka iya faruwa yayin hawan Sallah.
Kiran na zuwa ne bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bada umarni ga sarakunan jihar su shirya hawan Sallah, kuma rundunar ta yi alkawarin ba da kariya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng