Lagos Za Ta Sha gaban Kano da Katsina bayan Amincewar Kudirin Majalisa

Lagos Za Ta Sha gaban Kano da Katsina bayan Amincewar Kudirin Majalisa

  • Majalisar Wakilai ta amince da kudirin dokar da zai mayar da kananan hukumomi a Lagos guda 57 daga 20 da ake da su
  • Kudirin dokar, wanda wasu ‘yan majalisa 22 suka dauki nauyi, na daga cikin kudirori 42 da aka amince da su a ranar Laraba
  • Idan aka amince da kudirin, yawan kananan hukumomin Najeriya zai karu daga 774 zuwa 811, inda Lagos za ta fi sauran jihohi
  • Kano na da 44 yayin da Katsina ke da 34, amma dokar za ta tabbatar da Lagos a matsayin jiha mafi yawan kananan hukumomi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Majalisar Wakilai da ke birnin Abuja ta amince da kara wa jihar Lagos kananan hukumomi har guda 37.

Kudirin dokar na neman mayar da kananan hukumomin a jihar Lagos daga guda 20 zuwa 57.

Kara karanta wannan

Kuma dai: Majalisa ta kawo kudurin da zai hana Tinubu, Atiku, Obi yin takara

Majalisa ta amince da kudirin karawa Lagos yawan kananan hukumomi
An gabatar da kudirin da zai kara kananan hukumomin Lagos daga 20 zuwa 57. Hoto: House of Representatives.
Asali: Facebook

An gabatar da kudirin ƙirƙirar sababbin jihohi

The Guardian ta ce idan an kafa dokar, jimillar kananan hukumomin Lagos za su karu daga 20 zuwa 57.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan gabatar da kudirin kan shirin kirkirar sababbin jihohi guda hudu a Najeriya a yau Laraba 26 ga watan Maris, 2025.

Majalisar Wakilai ta amince da karatu na biyu na kudirori hudu da ke neman kirkirar sababbin jihohi a Najeriya.

An amince da wasu karin kudirori 38 da ke neman sauya kundin tsarin mulki na shekarar 1999.

Sababbin jihohin da ake so a kirkira su ne Oke-Ogun, Ijebu, Ife-Ijesa, Tiga, Orlu da Etiti domin hadewa da jihohi 36.

Lagos: An kawo kudiri domin kara kananan hukumomi

Wannan kudirin dokar yana daga cikin kudirori 42 da aka amince da su a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025.

‘Yan majalisa kamar Hon. James Abiodun Faleke da wasu 21 suka dauki nauyin kudirin a majalisar.

Kara karanta wannan

Kasar Saudiyya ta fitar da sanarwa kan duba watan sallar azumi

Sunan kudirin shi ne:

"Dokar Gyara Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) don amincewa da kananan hukumomin Lagos a matsayin cikakkun daga 20 zuwa 57."
Za a kara yawan kananan hukumomi a Lagos
Lagos za ta zamo jihar da tafi yawan kananan hukumomi a Najeriya. Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Asali: Twitter

Kananan hukumomi a Najeriya za su ƙaru

An amince da kudirin a karatu na biyu a ranar Laraba, lokacin da mataimakin kakakin majalisa, Benjamin Kalu, ya jagoranci zaman, cewar rahoton Punch.

Idan aka amince da kudirin ya zama doka, zai kara adadin kananan hukumomi daga 774 zuwa 811, wanda zai kara yawan wakilci a matakin jiha da tarayya.

Lagos za ta kasance jihar da ke da yawan kananan hukumomi mafi yawa a Najeriya, yayin da Kano da ke da 44 sai Katsina mai guda 34.

Dalilan da aka duba

Bayan amincewa da kudirin a karatu na biyu, wasu ‘yan majalisa sun yi bayani kan dalilan da suka sa suka goyi bayan karin kananan hukumomi a Lagos.

Hon. James Abiodun Faleke ya ce yawan jama’a a Lagos yana ƙaruwa da sauri, kuma dole ne a samu karin kananan hukumomi don inganta ayyukan gwamnati da samar da ci gaba mai dorewa.

Kara karanta wannan

Kariya ta kare: Majalisa ta amince da kudirin da zai tubewa ƴan siyasa zani a kasuwa

Sai dai, akwai sabani kan wannan kudiri, inda wasu ke ganin cewa Lagos na samun fifiko fiye da wasu jihohi.

Wani jigo a majalisar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa idan za a kara yawan kananan hukumomi a Lagos, to ya dace a yi la’akari da sauran jihohi da ke da bukatar karin yanki.

Bugu da ƙari, masana doka sun bayyana cewa kafin a aiwatar da kudirin gaba ɗaya, dole ne ya samu amincewar majalisar dattawa da kuma gwamnonin jihohi.

A yanzu, ana sa ran cewa majalisar za ta ci gaba da muhawara kan batun a matakin gaba, tare da fatan samun matsaya da za ta yi dai-dai da tsarin mulkin ƙasa.

Majalisa za ta cire kariya ga ƴan siyasa

Mun ba ku labarin cewa Majalisar wakilai ta amince da kudirin da ke neman cire kariya daga shari’a ga mataimakin shugaban kasa, gwamnoni da mataimakansu.

Kara karanta wannan

Maganar kirkirar sababbin jihohi ta dawo, kudirin ya tsallake karatu na 2 a majalisa

'Dan majalisa, Solomon Bob ne ya dauki nauyin kudirin domin hana rashawa, kawar da rashin hukunci da karfafa gaskiya a shugabanci na gari.

An ce kudirin ya na neman gyara sashe na 308 na kundin tsarin mulki, wanda ke kare shugabannin daga tuhuma ta shari’a a lokacin da suke kan mulki.

Salisu Ibrahim ya fadada wannan labarin ta hanyar kara bayani kan dalilin kara kananan hukumomi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng