Masu Bautar Kasa a Najeriya na cikin Alheri Dumu Dumu, Tinubu Ya Fara Biyan N77, 000
- Matasa masu yi wa ƙasa hidima na cikin alheri dumu dumu yayin da suka fara karɓar sabon alawus na N77,000 daga ranar Laraba, 26 ga Maris
- A farkon Maris, shugaban NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu, ya tabbatar da kudurin gwamnatin na fara biyan kudin a karshen wata
- Wasu 'yan NYSC da suka zanta da Legit.ng Hausa sun nuna farin ciki da fara karbar sabon alawus din, amma sun koka da jinkirin da aka samu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Daga wannan mako, jiran da matasa masu yi wa kasa hidima, watau NYSC suke yi na fara karbar sabon alawus din N77,000 ya kare.
Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta fara biyan masu bautar kasa N77,000 daga ranar Laraba, 26 ga Maris, 2027.

Kara karanta wannan
'Yara miliyan 1.5 za su mutu': Najeriya na fuskantar sabuwar barazana daga Amurka

Asali: Twitter
Alkawarin hukumar NYSC ga masu bautar kasa
Legit Hausa ta rahoto cewa, shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu, a makon jiya, ya ce gwamnati za ta fara biyan N77,000 daga Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana hakan ne a lokacin da gana da 'yan bautar kasa da ke aiki a ofisoshin NYSC na yankunan Wuse da Garki, a Abuja, babban birnin kasar nan.
Birgediya Janar Olakunle ya bayyana wa ƴan bautar ƙasa cewa:
"Daga watan Maris, za ku fara karɓar N77,000 a matsayin alawus na wata-wata. NYSC na da ingantaccen tsari na adana bayanai, kuma ina tabbatar muku cewa za a biya ku haƙƙokinku."
Ya ƙara da cewa, "Ƙasar nan da hukumar NYSC suna jin daɗin hidimar da kuke yi."
Har ila yau, ya jaddada cewa hukumar NYSC tare da gwamnatin tarayya na da alhakin kula da jin daɗin matasa, kuma za su ci gaba da ba da fifiko ga walwalarsu a kowane lokaci.
NYSC: Gwamnatin Tinubu ta cika alkawari
A zantawar Legit.ng da Hauwa'u Lawal, matashiya mai yi wa kasa hidima a Katsina, ta tabbatar da cewa ta karbi alawus dinta na N77,000 da misalin karfe 1:26 na rana.
Hauwa'u Lawal ta ce ba ta taba tsammanin za ta kasance a cikin wadanda za su amfana da N77,000 ba, saboda tsawon watanni shida ana sanya masu rai, ba a cika ba.
"Da na ga kudin sun shigo, sai da na murza idanuwa na, na kara kallon sakon, na tabbatar cewa eh daga bankin Zenith ne da na bude a sansanin NYSC.
"Na kira yayata na nuna mata, muka yi tsalle cikin murna, Allah ya ga ni, na ji dadin shigowar kudinta, saboda ina da bukatun da zan yi na Sallah."
Yayin da ta nuna damuwa kan jinkirin da aka samu na fara biyan kudin duk da amincewar Shugaba Tinubu, Hauwa'u ta ce:

Kara karanta wannan
2027: Ta fara tsami tsakanin ƴan adawa, burin Atiku da maganar yanki na son ta da kura
"Ni yanzu saura watanni uku na kammala, ka ga ba zan wani amfana da N77,000 din sosai ba, amma ina fatan gwamnati za ta cika alkawarin cikata mana kudin mu kamar yadda ta yi alkawari."
"Na ji dadi, ban ji dadi ba" - Rahama

Asali: Twitter
Ita ma Rahama Hamza, wadda ke shirin kammala bautar kasarta a ranar Juma'a, 28 ga Maris, ta shaidawa Legit Hausa cewa ta karbi na ta N77,000 din, tana mai cewa:
"Na ji dadi ban ji dadi ba, saboda ni sau daya zan samu N77,000 din. Ka ga fa tsawon watanni shida da muka yi ba a fara biya ba, sai da muka gama ne za su fara biya, ai ka ga mu ba mu da sa'a a lamarin.
"Na dan ci buri kan kudin, a lokacin da aka ce za a fara biya, ina ga Disamba ke nan, shekarar da ta wuce, amma tun da aka shiga Fabrairu, na cire rai ma kwata kwata."
Rahama Hamza ta yi wa masu shirin fara yi wa kasa hidima murnar shiga tsarin a lokacin da aka fara biyan sabon alawus din, tana mai shawartarsu a kan yin tattali.
Matashiya ta mutu a hanyar zuwa sansanin NYSC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata matashiya mai shirin yi wa ƙasa hidima ta rasa ranta sakamakon hatsarin mota yayin da take kan hanyarta zuwa sansanin NYSC a Ebonyi.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya rutsa da mutum 12 daga cikin masu shirin bautar ƙasa, sai dai ita kaɗai ce ta rasu a nan take.
Asali: Legit.ng