Ana tsakar Rikicin Sarauta da Hawan Sallah, Kwankwaso Ya Dura Kano da Tawagarsa
- Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sauka a jiharsa ta Kano domin yin bukukuwan sallah a gida
- Kwankwaso ya koma Kano ne a daidai lokacin da ake shirin hawan sallah, wanda Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado ke haramar yi
- Hadimin Kwankwaso na ɓangaren yada labarai, Saifullahi Hassan ya tabbatar da isar madugun Kwankwasiyya Kano a wata sanarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya dura jihar domin yin ƙaramar sallah da ke tafe a gida.
Kwankwaso ya koma mahaifarsa watau Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya a daidai lokacin da jama’a ke shirin gudanar da bikin sallah.

Asali: Twitter
Mai taimakawa Kwankwaso kan harkokin yaɗa labarai, Saifullahi Hassan ne ya bayyana hakan a wata gajeruwar sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rabiu Kwankwaso da tawagarsa sun isa Kano
Kwankwaso, wanda ke da magoya baya masu dimbin yawa a Kano da ma wasu sassan kasar nan, ya dawo garin ne domin yin bikin sallah tare da al’ummar jihar.
A sanarwar da Saifullahi ya fitar yau Laraba, 26 ga watan Maris, 2025 ya ce:
"Mai girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya dawo gida a jihar Kano yayin da muke shirye-shiryen bukukuwan ƙaramar sallah.
"Zuwansa da kasancewarsa a gida na ƙara karfafa al'ummar jihar Kano na haɗa kan jama'a, muna ma ku barka da ƙaramar sallah da ke tafe."
Kano: An fara surutu kan hawan sallah
Kwankwaso ya koma Kano ne a daidai lokacin da ake ta surutu kan hawan sallah da sarakuna biyu, Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero suka shirya.
Wannan lamari dai ya ƙara tsananta rikicin sarauta da aka jima ana fama da shi a jihar Kano, yayin da magoya bayan sarakunan ke ƙara jaddada cewa ba gudu ba ja da baya.
Mutane da dama a Kano na fargabar abin da ka iya zuwa ya dawo da yiwuwar ɓarkewar rigima idan har duka sarakunan suka fito yin hawan sallah.
Ana tsakiyar wannan ka-ce-na-ce ne kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta sake jaddada cewa kotun koli ce za ta raba gardama tsakanin Sanusi II da Aminu Ado.
Ana wannan batu ne, madugun Kwankwasiyya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP ya sauka a jihar Kano domin yin shagalin sallah a gida.
A yayin isowarsa, jama’a sun tarbe shi da farin ciki, inda da dama daga cikin mabiyansa ke bayyana gamsuwa da zuwansa.
Magoya bayan Kwankwaso sun ɗauki zafi
A wani labarin, kun ji cewa ƴan Kwankwasiyya sun yi ca kan wani Dr. Usman Isiyaku kan sukar shugabansu kuma jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso.
Usman ya caccaki Sanata Kwankwaso saboda jinkirin da ya yi wajen bayyana matsayarsa kan dokar ta ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya ƙaƙaba a jihar Ribas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng