Katsina: 'Yan Bindiga Sun Farmaki Bayin Allah cikin Azumi, an Samu Asarar Rayuka

Katsina: 'Yan Bindiga Sun Farmaki Bayin Allah cikin Azumi, an Samu Asarar Rayuka

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wani ƙauyen jihar Katsina inda ake kukan rashin tsaro
  • Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Tudu cikin ƙaramar hukumar Kankara a ranar Talata, 25 ga watan Maris 2025
  • A yayin harin, ƴan bindigan sun hallaka mutum biyu har lahira bayan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi haka kurum
  • Bayan samun rahoton kai harin, dakarun sojoji sun kawo ɗaukin gaggawa domin daƙile farmakin da miyagun suka kawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Tudu, da ke cikin ƙaramar hukumar Kankara a Jihar Katsina.

Ƴan bindigan sun hallaka mutum biyu a yayin harin wanda suka kai a ranar Talata, 25 ga watan Maris 2025.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina
'Yan bindiga sun kai hari a jihar Katsina Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan sanda sun dakile mugun nufin 'yan bindiga, sun kubutar da bayin Allah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai hari a Kankara

Majiyoyi sun bayyana cewa, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe, yayin da mazauna ƙauyen ke tsaka da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Waɗanda suka tsira daga harin sun ce ƴan bindigan sun zo ne a kan babura, ɗauke da makamai iri-iri, sannan suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Bayan samun rahoton harin, jami’an tsaro da ke karkashin rundunar Operation Fansan Yanma sun gaggauta tura dakaru domin daƙile farmakin da ƴan bindigan suka kawo.

Sai dai, kafin jami’an tsaro su isa wurin, ƴan bindigan sun riga sun hallaka wasu mazauna ƙauyen guda biyu da aka bayyana sunayensu a matsayin Nasiru Chinnaka da Kamilu Mamman.

Bayan kisan, ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da wasu kayayyaki daga cikin ƙauyen, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin tsananin fargaba da tashin hankali.

Irin waɗannan hare-hare sun zama ruwan dare a yankin, kuma suna barazana ga rayuwa da dukiyoyin jama’a.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun gwabza da 'yan bindiga, sun ceto mutanen da aka sace

Yan sandan Najeriya
Jami'an 'yan sandan Najeriya Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Jami'an tsaro sun ci gaba da sintiri a Katsina

An bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da sintiri a yankin don tabbatar da tsaro da kuma hana sake kai irin wannan harin.

Gawarwakin wadanda suka rasa rayukansu an ɗauke su zuwa babban asibitin Kankara.

Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kokarin dakile matsalar tsaro a jihar Katsina, inda jami’an tsaro ke ƙara ƙaimi wajen yaki da ƴan bindiga da masu tayar da zaune tsaye a yankunan karkara.

Ƴan sanda sun daƙile harin ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun samu nasarar daƙile harin ƴan bindiga.

Miyagun ƴan bindigan sun yi yunƙurin yin garkuwa da mutane a kan hanyar Funtua/Dandume bayan sun dawo daga kasuwa.

An ji cewa bayan samun rahoton mugun nufin na ƴan bindiga, ƴan sanda sun garzaya zuwa wajen inda suka fatattaki miyagun.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng