Hawan Sarakuna 2: Yadda Jama'a za Su Tunkari Bukukuwan Sallah a Jihar Kano
Bikin hawan Sallar Kano a bana jawo cece-kuce sakamakon umarnin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar, martanin Sarkin Kano na 15 watau Aminu Ado Bayero da kuma matsayar jama'ar gari.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Tun bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci dukkan masarautun Kano da su fara shirin gudanar da bikin hawan Sallah, wasu mazauna Kano suka shiga fargaba.
Tun bayan fara dambarwar masarauta ne aka samu cikas wajen gudanar da hawan Sallah na al'ada da aka saba yi a jihar, lamarin da gwamna ya ce zai sauya a bana.

Asali: Facebook
A sakon da Darakta Janar na yada labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a Facebook, gwamnan ya ce jami'an tsaro za su yi aikin kare rayuka a yayin hawan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin Sarki Aminu ga hawa a Kano
Jaridar Leadership ta wallafa cewa jim kadan da sanarwar gwamna Abba ne aka ga bangaren Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero, ya aika da wasika zuwa rundunar ‘yan sandan jihar.
A cikin wasikar, ya sanar da shirinsa na gudanar da nasa bikin hawan Sallah da suka hada da hawan Daushe da na Nassarawa, wanda aka tsara su a ranakun 1, 2, da 3 ga watan Shawwal 1446 AH.
Wannan lamari ya tsorata wasu daga cikin mazauna Kano, wadanda suka saba ganin rigingimun daba da kwace wayoyi a lokutan bukukuwan hawan Sallah.
'Yan sanda sun magantu kan hawa a Kano
Tuni aka fara samun masu shaida wa 'yan sanda fargabar abin da ka je ya zo, matukar aka bar sarakuna biyu masu adawa da juna su gudanar da hawan Sallah.

Asali: Facebook
A ziyarar da tawagar kungiyoyi masu zaman kansu su ka kai ofishi rundunar 'yan sandan Kano, sun shaida wa kwamishinan 'yan sandan, CP Ibrahim Adamu Bakori, cewa akwai matsala.
Amma kwamishinan ya bayyana masu cewa har yanzu ana tuntuba, koma za a dauki matakan kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Mutanen jihar Kano ba su gamsu ba
Wasu daga cikin mazauna Kano sun shaida wa Legit cewa ba da su za a gudanar da hawan karamar sallah ba, ko da hukumomi sun ba da tabbacin kare rayukansu.
Wata Hadiza Musa ta ce:
"Tab, mutum idan ya fita hawan Sallah ya yi wa kansa."
Muhammad Muhmmad ya ce:
"Wannan rabuwar kai na masarautu gaskiya ba zai haifar da da mai ido ba. Ba kowa ne da hankalinsa, ya na ganin ana wannan rigima tsakanin masarautu a Kano, kuma ya ce zai je kallon hawa. Ni ba za ni ba, kuma ba na fatan wani nawa ya je."
Ya shawarci jagororin da su duba wadanda su ke mulka, su ajiye gabar da ta ratsa tsakaninsu domi ci gaban talakawan da su ke son jagoranta.
Shamsu Umar ya ce:
"Ni gaskiya a hange na, mafi sauki a hakura da wannan hawa idan zai kawo cikas ga zaman lafiyar jihar Kano. Idan ba a manta a shekarun baya, an hana sallar Juma'a saboda korona kuma ba a yi ba, ina ga abin da ya sa ake so a samar da zaman lafiya?
A gani na gaskiya a hakura da wannan hawan, shi ne mafi a'ala ga mutanen jihar Kano.
Farida ta ce:
"Bana kowa ya na da zabi, kowa da sarkin da zai bi."
An roki Sarki Aminu ya bar hawan Sallah
A wani labarin, kun ji yadda malamin addinin Musulunci, Sheikh Lawan Abubakar Shu'aibu Triumph, ya bayyana damuwa game da halin da Kano za ta fuskanta idan aka gudanar da hawan Sallah biyu.
Ya roki Sarkin Kano 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da ya dubi Allah, ya ajiye batun gudanar da hawan Sallah, wanda a ganinsa, wannan mataki zai kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng