"Ku Shirya," Sheikh Abdullahi Pakistan Ya Hango Matsalar da Za a Fuskanta a Aikin Hajjin 2025
- Shugaban hukumar kula da maniyyatan Najeriya watau NAHCON, Abdullahi Pakistan ya ce da yiwuwar a fuskanci zafin rana a hajjin bana
- Sheikh Pakistan ya gargaɗi masu shirin sauke farali a 2025 su shirya fuskantar zafin rana mai tsanani yayin da hukumar ta ke nata shirye-shiryen
- Ministam lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya ziyarci NAHCON a Saudi domin duba matakai da kayayyakin da aka tanada don kula da lafiyar maniyyata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar Kula da Harkokin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta gargadi maniyyata da su yi shirin fuskantar zafin rana mai tsanani a lokacin aikin Hajjin 2025.
Shugaban NAHCON, Sheikh Abdullahi Saleh Usman Pakistan ne ya yi wannan gargaɗin yayin da ya karɓi bakuncin ministan lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate.

Asali: Facebook
Sheikh Abdullahi Sale ya jagoranci ministan lafiya wajen duba kayayyakin aikin hukumar NAHCON a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban NAHCON ya gargaɗi maniyyata
A cikin wata sanarwa, shugaban NAHCON ya jaddada muhimmancin shirin kula da lafiyar maniyyata, la’akari da yawan ‘yan Najeriya kimanin 70,000 da ke aikin hajji kowacce shekara.
Ya ce matsalar sauyin yanayi da ke haddasa zafin rana mai tsanani na da matukar tasiri, kuma NAHCON ta himmatu wajen daukar matakan kariya don kiyaye lafiyar maniyyata.
Wane tanadi gwamnati ta yi domin aikin hajji?
A nasa jawabin, Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate, ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta dauki duk matakan da suka dace don magance matsalolin lafiya da maniyyata ke fuskanta.
Ya ce gwammati ta tattauna da hukumar NAHCON domin ganin an yi ingantaccen shirin kare lafiyar maniyyata a lokacin da suka tafi aikin hajjin bana.
“Tattaunawarmu da hukumar NAHCON ta nuna aniyar gwamnati na ɗaukar matakan ƙare lafiyar maniyyata ƴan asalin Najeriya.
"Idan aka duba matsalolin kiwon lafiya na duniya, kamar yaduwar cutar sanƙarau da shan inna, dole ne mu cika ka’idojin kiwon lafiya na ƙasar Saudiyya."

Kara karanta wannan
"Ba ni da hannu," Sheikh Sulaimon ya fashe da kuka a tafsirin Ramadan, ya rantse da Alƙur'ani
- In ji Farfesa Muhammad Pate.

Asali: Twitter
Hajjin 2025: Za a yi wa maniyyata rigakafi
Ministan ya kara da cewa dole ne duka maniyyata su mallaki takardar shaida ta yin rigakafi kafin tafiya, domin gujewa matsaloli a ƙasar Saudiyya.
"Dole mu tabbatar kowane ɗan Najeriya da zai zo aikin hajji yana da takardun rigakafi wanda ya haɗa da katin shaida domin cika ƙa'idoji," in ji shi.
Farfesa Muhammad Pate ya kuma duba motocin ujila, masu kai ɗauki ga marasa lafiya idan bukatar hakan ta taso, kamar yadda Guardian ta ruwaito.
Bugu da ƙari, ministan ya duba kayayyakin kula da lafiya, cibiyoyin kiwon lafiya da hukumar NAHCON ta tanada domin jin daɗin maniyyatan Najeriya a Saudiyya.
NAHCON za ta fara jigilar hajji a watan Mayu
A wani labarin, kun ji cewa hukumar NAHCON ta bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa na fara jigilar maniyyata daga Najeriya zuwa kasa mai tsarki a Mayu.
NAHCON na aiki kafaɗa da kafaɗa da kamfanonin jiragen sama domin sauƙaƙa jigilar Alhazai 75,000 daga jihohi daban-daban na ƙasar nan zuwa Saudiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng