Babban Malami Ya Hango Matsala a Kano, An Nemi Alfarmar Sarki kan Hawan Sallah
- Fitaccen malamin addinin Musulunci, Lawan Abubakar Shu'aibu Triumph, ya bayyana damuwa game da yiwuwar gudanar da hawan Sallah biyu a Kano
- Sheikh Triumph ya bayyana cewa gudanar da hawan Sallah biyu zai iya jawo fitina da zubar da jini a Kano, musamman bayan an kammala ibadar azumi
- Ya yi kira ga Aminu Ado Bayero a kan ya dauki matakin da zai kare rayuka da dukiyoyin mazauna jihar a lokacin da ake murnar bikin Sallah a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Lawan Abubakar Shu'aibu Triumph, ya bayyana damuwa kan halin da Kano za ta shiga idan aka yi hawan Sallah biyu.
Fargabarsa ta taso ne yayin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta umarci hakimai da dagatai da su fito domin gudanar da hawan Sallah karama tare da kai gaisuwa ga Muhammadu Sanusi II.

Asali: Facebook
A wani bidiyo da Muhd Gagara ya wallafa a shafin Facebook, Sheikh Triumph ya bayyana cewa sun samu labarin umarnin gwamna ga sarakunan Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce sun kuma ji cewa bangaren Sarkin Kano na 15, Mai Martaba Aminu Ado Bayero, ya samu sahalewar jami'an tsaro domin gabatar da hawan Sallah.
Ana fargabar hawan Sallah biyu a Kano
Sheikh Lawan Abubakar Shu'aibu Triumph ya bayyana rashin jin daɗin kokarin gudanar da hawan Sallah biyu, lamarin da ya ce zai iya jawo zubar da jinin bayin Allah.
Malamin ya ce:
"Idan an tafi a haka, ba fata muke ba, ke nan mu mutanen Kano, Juma'armu za ta kare a Laraba, Sallarmu za ta zama akwai fitina, akwai matsala, akwai tashin hankali."
"Ba ga kanka ba ma, ga wani dan uwanka Musulmi ba za ka so wannan ya faru gare shi ba. A ce an gama ibadar azumi, za a yi murnar bukukuwan Sallah, amma a tashi da rikici da hatsaniya."
An nemi alfarma kan hawan Sallah
Malamin addinin Musulunci ya roki Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, da ya fasa hawan Sallah domin kare martaba da rayukan talakawan Kano.

Asali: Facebook
Sheikh Triumph ya bayyana cewa idan an dakatar da ɗaya daga cikin hawaye, za a samu damar tabbatar da zaman lafiya a Kano da kuma hana afkuwar fitina.
Ya ce:
"Musamman ga bangaren Mai Martaba Sarki Aminu, su kalli Allah su yi hakuri. Ana shaidarsa a matsayin mutum mai son zaman lafiya, wanda ba ya da abokin faɗa, har ma makiyansa suna tabbatar da hakan."
"To, mu na rokon wannan afarma ga wannan bangare. Su kalli Allah, su tsare rayukan al’umma, su janye don a zauna lafiya."
An yi wa tsohon Sarkin Kano addu’a
Malamin ya yabawa halayen marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, yana mai cewa ana da tabbacin Sarki Aminu ya gaje shi.
Ya bayyana fatan cewa tsagin Aminu za su nuna dattako tare da halaye irin na marigayi, Alhaji Ado Bayero.
Ya ce:
"Muna fatan Mai Martaba Sarki ya yi hakuri. Allah Madaukakin Sarki ya ji kan Sarki Ado, kuma ya kawar da duk wani abu mara kyau."
'Yan sanda sun magantu kan hawan Sallah
A baya, kun samu labarin cewa rundunar 'yan sandan Kano ta bukaci jama'a da su yi hattara da duk wani abu da zai iya haifar da tashin hankali ko rikici a lokacin bikin karamar Sallah.
Wannan kiran ya zo ne a daidai lokacin da ake zaton Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II da Aminu Ado Bayero za su gudanar da hawan Sallah daban-daban a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng