Tsadar Rayuwa: Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli Ya Samo Mafita ga Magidanta
- Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli ya yi magana kan halin tsadar rayuwa da ake fama da shi a ƙasar nan
- Mai martaba sarkin ya buƙaci magidanta masu ƙaramin ƙarfi da ka da su auri mace fiye da ɗaya domin su samu damar sauke nauyin da ke kansu
- Ya koka da yadda mutane suke tara ƴaƴa masu yawa duk da ba su da sukuni ko wadatar da za su iya kula da su yadda ya dace
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, ya ba magidanta shawara kan halin matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi a ƙasar nan.
Sarkin na Zazzau ya buƙaci magidanta masu ƙaramin ƙarfi da su riƙa tsayawa da mace ɗaya domin su gina iyalai masu inganci.

Asali: Facebook
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wajen rufe karatun tafsirin Ramadan na shekara-shekara karo na 30 na ƙungiyar mata musulmi ta Najeriya (FOMWAN), cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya koka kan yadda auren mata fiye da ɗaya ke ruguza iyalai saboda magidanta sun gaza sauke nauyin da ke kansu.
Wace shawara Sarkin Zazzau ya ba da?
Mai martaba sarkin ya ce, duk da cewa addinin Musulunci ya ba wa maza damar auren mace fiye da ɗaya, hakan ba yana nufin kowane namiji na da ikon ɗaukar nauyin iyalansa ba.
"A fada, akwai iyalai 192 da ke zaune a ciki, kuma daga cikinsu za ka ga mutum ɗaya yana da sama da ƴaƴa 50. Ta yaya zai iya ɗaukar nauyinsu?"
- Mai martaba Ahmed Nuhu Bamalli
Sannan ya buƙaci a sake duba tsarin karatun Islamiyya domin a riƙa koyar da haƙƙoƙin mata a Musulunci.
Mai martaba Sarkin na Zazzau ya ce hakan zai canza tunani da kuma gina al’umma mai kyau.

Asali: Facebook
Ya zargi alƙalai da ƙara dagula matsalolin al’umma, inda ya bayar da misalin wata mata da aka yankewa hukuncin ɗauri na shekaru biyu saboda ta kasa biyan bashin N6,000.
“Ranar da na je gidan yari, Naira 200,000 kawai na ke da ita a hannuna, amma da ita na samu aka saki mutane takwas."
- Mai martaba Ahmed Nuhu Bamalli
An buƙaci malamai su tunatar da magidanta
A nata jawabin, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta buƙaci malamai da su ƙarfafawa magidanta gwiwa su ɗauki nauyin iyalansu kamar yadda Allah ya ɗora musu.
“Dole malamai su dage wajen faɗakar da magidanta su ɗauki nauyin gidajensu, domin an gano cewa a yanzu mafi yawan ɗawainiyar gida tana kan mata."
- Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe
Kotu ta raba gardama kan sarautar Zazzau
A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara ta zartar da hukunci kan ƙarar da ke neman a tsige Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta yi watsi da.ƙarar wacce ta nemi a soki naɗin da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai, ya yi wa Sarkin a shekarar 2020.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng