2027: 'Yan Majalisa na Kwaskware Tsarin Zaben Shugaban Kasa da Gwamnoni

2027: 'Yan Majalisa na Kwaskware Tsarin Zaben Shugaban Kasa da Gwamnoni

  • Rahotanni na nuna cewa majalisar wakilai ta yi karatu na biyu ga kudirin dokar da ke neman gudanar da dukkan zaɓuka a rana guda
  • Kudirin ya tanadi cewa zaɓen shugaban ƙasa, gwamna, ‘yan majalisar dokoki da kananan hukumomi su kasance a rana ɗaya
  • Majalisar ta kuma karanta wani kudiri da ke neman kotun ɗaukaka ƙara ta zama matakin ƙarshe wajen sauraron ƙarar zaɓen gwamna

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A zaman ta na ranar Talata, Majalisar Wakilai ta amince da kudirin dokar da ke neman a gudanar da dukkan zaɓuka a rana guda a Najeriya a matakin karatu na biyu.

Kudirin da Hon. Ikenga Ugochinyere da Hon. Francis Ejiroghene Waive tare da wasu ‘yan majalisa 34 suka gabatar, ya samu goyon bayan yawancin ‘yan majalisar.

Kara karanta wannan

Tankar mai ta sake fashewa a Neja, hukumomi sun tashi tsaye

Majalisa
Majalisa ta yi karatu na 2 ga kudirin sauya tsarin zabe. Hoto: House of Representative, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa an gabatar da kudirin ne don karatu na biyu ta hannun Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Hon. Julius Ihonvbere.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan har majalisar ta masa karatu na uku kuma ya samu amincewar majalisar zartarwa karkashin Bola Tinubu, zai iya fara aiki a zaben 2027.

INEC za ta rika tantance ranar zaɓe

Sabon kudirin dokar na neman sauya wasu sashe na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 domin tabbatar da cewa dukkan zaɓuka su kasance a rana guda.

A cewar kudirin, hukumar zaɓe ta INEC ce za ta tantance ranar gudanar da zaɓen tare da shawarar Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Vanguard ta wallafa cewa kudirin ya tanadi cewa zaɓen Shugaban Ƙasa, gwamnoni, ‘yan majalisar tarayya, ‘yan majalisar jiha da kansiloli za su gudana rana guda.

Gyaran tsarin sauraron ƙarar zaɓe a Najeriya

Bayan amincewa da kudirin, Majalisar Wakilai ta kuma karanta kudirin dokar da ke neman kotun ɗaukaka ƙara ta zama matakin ƙarshe wajen sauraron ƙarar zaɓen gwamna.

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

Kudirin da Hon. Nnamdi Ezechi ya gabatar na neman gyara sashen 246 na kundin tsarin mulki, domin ba wa kotun ɗaukaka ƙara cikakken iko a ƙarar zaɓen gwamna.

Yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamna

A yanzu, sashen 246 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanadi cewa hukuncin kotun ɗaukaka ƙara kan shari’ar zaɓen ‘yan majalisar dokoki na jiha da tarayya shi ne matakin ƙarshe.

Sabon kudirin dokar na son a yi gyara domin wannan tanadi ya haɗa da shari’ar zaɓen gwamnoni, domin hana kai irin wannan ƙara zuwa kotun koli.

'Yan Najeriya dai za su zuba ido domin ganin yadda majalisar za ta yanke hukuncin karshe kan kudurorin yayin da shirye shiryen zaben 2027 ke fara kankama.

Majalisa
Yan majalisar wakilai yayin zama. Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Facebook

Alkali ya fita daga shari'ar 'yan majalisa

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi korafi kan shari'arsa da ake yi da Sanata Natasha Akpoti.

Alkalin da ke sauraron karar ya zare hannu a shari'ar bayan ya ce Sanata Akpabio ya yi korafin cewa ba lallai ya masa adalci ba a kan zargin da ake masa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng