Jagora a SDP Ya Samu Bakin Magana,Ya Yi Kaca Kaca da Salon Mulkin Tinubu

Jagora a SDP Ya Samu Bakin Magana,Ya Yi Kaca Kaca da Salon Mulkin Tinubu

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a SDP, Adewole Adebayo, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu saboda zargin gazawarta
  • Adebayo ya bayyana cewa Najeriya na fama da matsalolin talauci, rashin tsaro, da rashin doka da oda yayin da ake karfafa a Ribas
  • Ya nuna damuwarsa game da halin da Najeriya ke ciki, ya nacewa talauci da rashin ci gaba sun karu, duk da yalwar albarkatun ƙasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, tare da bayyana gazawarta a bangaren tsaro da tattalin arziki.

Da yake magana a Ilorin, jihar Kwara yayin bude baki, Adebayo ya caccaki shekaru biyu da Bola Tinubu ya yi yana mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

Tinubu
An caccaki salon mulkin Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Adewole Adebayo ESQ
Asali: Facebook

Jaridar Vangaurd ta wallafa cewa tsohon dan takarar ya ce Najeriya na fama da rashin tsaro, matsin tattalin arziki, da kuma rashin doka da oda a majalisar dokoki da jihar Ribas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tinubu ya yi abin kunya," 'Dan takaran SDP

Adebayo ya ce da dama daga cikin 'yan Najeriya sun yi zaton gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta tabuka abin arziki, amma ta ba da kunya.

Ya ƙara da cewa:

"Abin kunya ne a ce a ƙasar da Allah ya albarkace ta da yalwar arziki, amma talakawa ba su da abinci. A halin da ake ciki yanzu, mu na magana ne kan talauci, rashin tsaro, rashin ci gaba, rashin aikin yi. Wasu na son mulki ko ta wace hanya, har su haɗa kai da shaiɗan kawai don cimma burinsu."

Ya kuma soki yanayin hanyoyin Najeriya, yana mai cewa, tun da suka taso daga Ondo zuwa Kwara jikinsu ya ke gaya masu saboda tsananin rashin kyawun hanyar.

Kara karanta wannan

Ribas: Tambuwal ya tona yadda aka yi watsi da doka a majalisa don biyan buƙatar Tinubu

Dan takarar SDP a 2023 ya ce Tinubu ya gaza

Adebayo ya ce matsalar talauci da rashin ci gaba na kara ta’azzara, ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyar masu zuwa, yawan ‘yan Najeriya zai karu da 10%, amma babu aikin yi.

Adewole
Tsohon dan takarar shugaban kasa a SDP Hoto: Adewole Adebayo ESQ
Asali: Facebook

Ya kuma soki tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya na mai cewa;

"Buhari ya fito a talabijin yana cewa ‘Ku tafi gona’. Amma bai samar da filaye ba, bai samar da tsaro ba, bai kuma samar da taki ba."

An soki Tinubu kan dokar ta-baci a Rivas

Tsohon dan takarar shugaban kasar nan, Adewole Adebayo, ya ce babban abin takaici ne da kuma rashin adalci yadda Shugaba Tinubu ya wargaza tsarin dimokuraɗiyya a jihar Ribas.

Ya ƙara da cewa:

"Ya cire shugabanni da aka zaɓa a majalisa da kuma bangaren zartarwa. Wannan ya saba wa kundin tsarin mulkin ƙasa. ‘Yan siyasa a Ribas su sani cewa ikon mulki na hannun jama’a, kuma ya kamata a warware matsalar nan take."

Kara karanta wannan

Rikicin Ribas: An ƙara samun bayanai kan dalilin shugaba Tinubu na dakatar da gwamna

Haka kuma ya caccaki 'yan majalisa, ya ce:

"Ba su da muhimmanci a yanzu. Sun amince da kasafin kuɗi na ₦55trn ba tare da wata fa’ida ga talakawa ba. A bara ma sun amince da ₦40trn, amma babu wanda ya ga wani abu da aka yi da shi."

SDP ta shirya kwace mulki a hannun Tinubu

A wani labari, kun ji cewa shugaban SDP na ƙasa, Shehu Gabam, ya bayyana cewa jam'iyyar su na ci gaba da samun karɓuwa daga manyan 'yan siyasa daga dukkanin jihohin Najeriya.

A cewar Shehu Gabam, kowace rana akwai sababbin mutane da ke sauya sheka zuwa SDP, ciki har da manyan 'yan siyasa da suka riƙe muƙamai daban-daban a gwamnatin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng