Rundunar Ƴan Sanda Ta Yi Magana kan Shirin Hawan Sarakuna 2 a Kano
- Wasu daga cikin mazauna Kano sun fara bayyana fargabar halin da za a shiga idan sarakuna biyu suka gudanar da hawan Sallah
- Gwamnatin Kano ta umarci sarakunan da ta naɗa da su sayo sababbin dawakai, su yi hawan Sallah, a gaishe da Muhammadu Sanusi II
- A gefe guda kuma, tsagin Sarkin da gwamnati ta sauke, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya tabbatar da cewa za su gudanar da na su hawan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rundunar 'yan sandan Kano ta bukaci jama'a da su yi hattara don kauce wa duk wani tashin hankali ko rikici da ka iya faruwa a lokacin bikin karamar Sallah.
Kiran na zuwa a daidai lokacin da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya umarci sarakuna hudu na jihar su shirya hawan Sallah, yayin da Sarki Aminu Ado Bayero ma ya ce zai yi hawa.

Asali: Facebook
Sakon da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce Kwamishinan 'yan sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce ana shiri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya fadi haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga Kungiyoyi masu zaman kansu a jihar, a karkashin jagorancin Dr. Musa Sufi, a ofishinsa.
Kano: An shiga damuwa kan hawan Sallah
A yayin ziyarar, tawagar ta bayyana damuwa kan yanayin tsaro a Kano, musamman a lokutan bukukuwan hawan Sallah.
Tawagar ta ce an shiga samuwar da ta fi ta baya, saboda hasashen tashe-tashen hankula da za a samu biyo bayan hawan Sallah daga sarakuna biyu a lokaci guda
Martanin ƴan sandan Kano kan hawan Sallah
Da yake mayar da martani kan damuwarsu, CP Bakori ya tabbatar wa al'ummar Kano cewa rundunar 'yan sanda tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun shirya.

Asali: Facebook
Ya ce:
"Mun samu labari cewa wasu na shirin gudanar da bukukuwan Sallah daban-daban a lokaci guda, wanda hakan na iya haifar da tashin hankali.
Don haka, muna sake tsara dabarun tsaro, muna tattaunawa da masu ruwa da tsaki, tare da daukar matakan da suka dace don tabbatar da zaman lafiya."
Hawan Sallah: Ana neman hadin kan mutanen Kano
Kwamishinan 'yan sanda ya bukaci al'ummar Kano da su zama masu son zaman lafiya, su kasance cikin shiri, tare da kai rahoton duk wani abu da ba su gamsu da shi ba.
CP Bakori ya ce:
"A yayin da muke bikin wannan rana mai albarka, dole ne mu tuna cewa zaman lafiya shi ne babban ginshiki. Dole ne mu manta da bambance-bambancenmu, mu dunkule wuri guda domin ci gaban jihar Kano da kasa baki daya."
Rundunar ta jaddada aniyarta ta tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali, tare da bukatar hadin kan kowa da kowa domin samun bukukuwan Sallah cikin lumana.
Kira ga mazauna Kano
Bugu da ƙari, kwamishinan ya yi gargadi cewa duk wanda aka samu da laifin rura wutar rikici ko yaɗa jita-jita zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Ya ce gwamnati tana da cikakken iko na tabbatar da doka da oda, kuma ba za ta lamunci duk wani yunkuri na dagula zaman lafiya ba.
Haka nan, wasu masu fashin baki sun yi hasashen cewa rikicin masarautar Kano na iya shafar harkokin tattalin arzikin jihar, musamman kasuwanci da harkokin sufuri.
Wasu 'yan kasuwa sun fara bayyana damuwa kan yadda rashin tabbas ke hana su gudanar da harkokinsu yadda ya kamata.
A gefe guda, wasu kungiyoyin farar hula na kokarin shiga tsakani don ganin an samu maslaha. Kungiyar dattawan Arewa da wasu shugabannin addini sun yi kira da a guji furucin da ka iya kara rura wutar rikici.
Bayan haka, an samu rahotannin cewa jami’an tsaro sun kara tsaurara matakan tsaro a wasu yankunan Kano don kauce wa duk wani yunkuri na tayar da tarzoma.

Kara karanta wannan
Kaduna: Sarki ya samu shirgegen muƙamin gwamnati, Gwamna Uba Sani ya taya shi murna
Ana sa ran cewa gwamnati da sauran bangarorin da ke da ruwa da tsaki za su ci gaba da tattaunawa don magance matsalar ba tare da an kai ga rikici ba.
Aminu Ado Bayero ya duba filin hawan Sallah
A baya, mun wallafa cewa rikicin sarauta a Kano na kara kamari yayin da manyan sarakuna biyu ke ci gaba da shirin gudanar da hawan karamar Sallah a jihar.
Sarki na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ɗauki hankula, bayan an hango shi ya na rangadin filin idi, duk.kuwa da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba ta ɗauke shi Sarki ba.
Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng