Taimako ko Neman Suna: Najeriya Ta Tura Sojoji Wanzar da Zaman Lafiya Kasar Waje

Taimako ko Neman Suna: Najeriya Ta Tura Sojoji Wanzar da Zaman Lafiya Kasar Waje

  • Najeriya ta tura sojoji kimanin 171 zuwa Abyei, iyakar Sudan da Sudan ta Kudu, domin aikin wanzar da zaman lafiya karkashin shirin UNISFA
  • Manjo-Janar Boniface Sinjen ya bukaci sojojin su kasance masu da’a, tare da kaucewa duk wani abu da ka iya lalata martabar Najeriya
  • Rahoto ya nuna cibiyar MLAILPKC ta horar da sama da sojojin Najeriya 100,000 da suka je wanzar da zaman lafiya a kasashen da ake rikici

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da tura sojoji 171 zuwa Abyei, yankin da ke kan iyakar Sudan da Sudan ta Kudu, domin aikin wanzar da zaman lafiya.

Babban jami’in ayyuka na rundunar sojojin Najeriya, Manjo-Janar Boniface Sinjen, ne ya bayyana hakan a wurin bikin yaye sojojin da za su shiga aikin.

Kara karanta wannan

Rundunar sojojin saman Najeriya ta saki bama bamai a Borno, an hallaka 'yan ta'adda

Rundunar sojojin Najeriya ta yi magana da ta tura sojoji 171 zuwa Sudan wanzar da zaman lafiya
Najeriya ta tura dakarun sojoji zuwa kasar Sudan don wanzar da zaman lafiya. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

An tura sojojin Najeriya wanzar da zaman lafiya

Taron ya gudana ne a cibiyar koyar da shugabanci da ayyukan wanzar da zaman lafiya ta Martin Luther Agwai (MLAILPKC) da ke sansanin sojoji na Jaji, Kaduna, inji Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo-Janar Sinjen, ya jaddada muhimmancin aikin, ya na mai cewa aikin soja bai ta'allaka kan yaki da 'yan ta'adda kadai ba, su na shiga harkar diflomasiyya.

Ya bayyana cewa Najeriya na da kima a fannin aikin wanzar da zaman lafiya, inda sojojinta ke taka muhimmiyar rawa a kasashen da ke fama da rikici.

A cewarsa, yanayin tsaro a yankin Abyei na kara tabarbarewa, saboda rikice-rikicen kabilanci, hare-haren 'yan ta'adda, da matsalolin jin kai da ke addabar yankin.

Ya bukaci sojojin su kasance masu da’a, adalci, da girmama ‘yancin dan Adam yayin gudanar da aikinsu a karkashin hukumar tsaron wucin gadi ta Majalisar Dinkin Duniya (UNISFA).

Kara karanta wannan

Kaduna: Sarki ya samu shirgegen muƙamin gwamnati, Gwamna Uba Sani ya taya shi murna

An gargadi sojojin Najeriya da za a tura Sudan

Manjo-Janar Sinjen ya nanata cewa Majalisar Dinkin Duniya ba ta yarda da cin zarafin mata da yara ta hanyar lalata da su ba, tare da gargadin hukunci mai tsauri ga wadanda aka kama.

Ya shawarci sojojin da su kasance masu taka tsan-tsan, yin aiki tare, da kuma gudanar da ayyukansu da kima da mutunci domin kare martabar Najeriya a idon duniya.

Sinjen ya godewa kwamandan cibiyar MLAILPKC, Manjo-Janar Ademola Adedoja, da tawagar horarwar saboda kokarinsu wajen shiryawa sojojin wannan muhimmiyar tafiya.

An horar da sojoji 10,000 a cibiyar MLAILPKC

Shugabannin sojoji sun gargadi dakarun da aka tura Sudan wanzar da zaman lafiya
An horar da sama da sojojin Najeriya 10,000 da aka tura su aikin wanzar da zaman lafiya a kasashen duniya. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

A nasa jawabin, Manjo-Janar Adedoja ya ce yaye sojojin da aka yaye alama ce ta babban ci gaba, yayin da Najeriya ke tura dakarunta domin samar da zaman lafiya a duniya.

The Nation ta rahoto Janar Adedoja ya bayyana cewa cibiyar MLAILPKC ta horar da sama da sojoji 100,000, wadanda suka yi aiki a Liberia, Darfur, Saliyo, Gambiya, Guinea-Bissau da Abyei.

Kara karanta wannan

'Ayi hankali': Abin da shugaban rikon kwarya ya fada bayan shiga ofis a Rivers

A cewarsa, wannan nasara ta nuna dadadden kudurin Najeriya wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, tare da tallafa wa shirin Majalisar Dinkin Duniya.

Ya ce ya na da tabbacin cewa rundunar da aka yaye za ta ci gaba da kare wannan martaba, ta kuma taka muhimmiyar rawa a aikin UNISFA a yankin Abyei.

An tura sojojin Najeriya zuwa Gambiya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Najeriya ta tura sojojinta zuwa kasar Gambiya domin taimaka mata wajen wanzar da zaman lafiya da kare al'umma.

An ce akalla sojoji 197 ne aka ba su horo na musamman domin sanin aikin da za su je yi a kasar da ke fama da matsalolin tsaro daban-daban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng