Kano Ta Ɗauki Zafi da Kwamishinan Abba Ya Sa Ƴan Sanda Suka Tsare Wasu Ƴan Jarida
- Kungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da zargin tsare ƴan jarida biyu a Kano, bisa umarnin kwamishinan watsa labarai na jihar
- An ce an tsare ƴan jaridar ne saboda wallafa wata wasika da aka aikawa Gwamna Abba Yusuf ta da ke neman ya yi hattara da kwamishinan
- Kano ta dauki zafi kan lamarin, ƴan jarida kamar Jaafar Jaafar suka soki matakin da Ibrahim Waiya ya dauka, tare da kiran hakan 'zalunci'
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da kwamishina a Kano ya sanya aka tsare ƴan jarida biyu, Buhari Abba Rano da Isma'il Auwal.
Amnesty International ta yi ikirarin cewa kwamishinan watsa labarai na Kano, Ibrahim Waiya, ya sa an tsare matasan a ofishin ƴan sanda na tsawon awanni.

Asali: Facebook
Amnesty ta yi Alah-wadai da tsare 'yan jarida
A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook, kungiyar ta ce abin da kwamishinan ya yi, cin zarafi ne da barazana ga matasan ƴan jaridar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce:
"Buhari Abba, wanda edita ne na jaridar Kano Times, ya samu gayyata zuwa ofishin ƴan sanda (CIID) na Kano, inda aka tsare shi na tsawon awanni.
"Duk wadannan cin zarafi da barazanar sun faru ne saboda an wallafa wani ra'ayin Isma'il Auwal a shafin Kano Times.
"A sani cewa, bayyana ra'ayi bai taɓa zama laifi ba. Yunkurin gurfanar da ƴan jaridar bisa laifin bata suna ya nuna cewa ba a mutunta ƴancin fadar albarkacin baki ba."
Amnesty International ta nemi gwamnatin Kano da ƴan sandan Najeriya da su mutunta ƴancin kowa na fadar albarkacin baki, tana mai cewa:
"Ya zama wajibi a kawo ƙarshen yunƙurin amfani da ƴan sanda domin hukunta Buhari Abba da Isma'il Auwal, sannan a kare ƴancin su da dokar ƙasa ta ba su."
Kano: Me ya jawo 'yan sanda suka tsare ƴan jaridar?
Da Legit.ng ta bibiyi lamarin, ta gano cewa Ismail Auwal, ya rubuta wata budaddiyar wasika ne ga Gwamna Abba Kabir, wadda aka wallafa a jaridar Kano Times.
A cikin wasikar, mai taken: 'Abba Yusuf, ka yi hattara da kwamishinan watsa labaran Kano, Ibrahim Waiya," Isma'il ya gargadi gwamnan Kano da cewa:
"Idan har manufarka ita ce nada wakili, wanda zai toshe baraka tsakanin gwamnati da wadannan kungiyoyi, to akwai abin dubawa sosai.
"Ranka ya dade, Ibrahim Waiya ba shi ne mutumin da ya kamata ka ba irin wannan aiki ba. Akwai hazikan mutanen da ka ke tare da su, da za su magance matsalar ba tare da jawo wata matsalar ba."
An rahoto cewa, wannan wasika da Isma'il Auwal ya aikawa Gwamna Abba, ta harzuka kwamishinan, saboda ya na kallonta matsayin barazana ga muƙamin da ake shirin ba shi.

Kara karanta wannan
Natasha: Fada ya barke a majalisa, an yi kaca kaca tsakanin sanata da tsohuwar minista
An soki kwamishinan Kano kan tsare ƴan jarida

Asali: Facebook
Ɗan jaridar nan, Jaafar Jaafar, ya caccaki kwamishinan watsa labaran Kano, Ibrahim Waiya kan musgunawa ƴan jaridar ta hannun ƴan sanda.
A martanin da ya yi a shafinsa na Facebook, Jaafar Jaafar ya ce:
"Wai me aka ce ne a kan kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Ibrahim Waiya, da har zai sa a kama hazikin ɗan gwagwarmaya Ismail Auwal da editan jaridar Kano Times, Buhari Abba?
"Na tuntubi Ismail Auwal kan wannan gayyata da ƴan sanda su ka yi masa a kan ya ba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf shawarar cewa bai kamata Waiya ya jagoranci kwamitin tantace kungiyoyin NGOs na jihar Kano ba.
"Dalilin Ismail shi ne Waiya ya na da matsala da wasu kungiyoyin NGO a Kano, kuma a sanadiyar hakan yasa har ta kai yanzu haka ana shari’u kimanin uku akan rikice-rikicen.
"To menene laifi a wannan shawara da Ismail ya bayar? Wannan abin da kwamishina ya yi bai dace ba, kuma zalunci ne ƙarara."
Kwamishinan Kano ya yi murabus
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kwamishinan kula da ayyukan gwamnati a jihar Kano, Injiniya Muhammad Diggol, ya yi murabus daga mukaminsa.
Ya sauka daga kujerarsa ne a daidai lokacin da ake shirin rantsar da sababbin kwamishinonin da majalisar dokokin Kano ta amince da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng