Mutane Sun ga Abin Al'ajabi da Wani Bawan Allah Ya Rasu a Masallaci bayan Sallar Asuba

Mutane Sun ga Abin Al'ajabi da Wani Bawan Allah Ya Rasu a Masallaci bayan Sallar Asuba

  • Allah Ya karɓi rayuwar wani bawan Allah mai suna Rayyanu a cikin masallaci bayan sallar asubah ranar Talata a birnin Abuja
  • Marigayin ya kishingiɗa domin ya ɗan huta bayan sallame sallah, daga bisani rai ya yi halinsa a karamar hukumar Gwagwalada
  • Lamarin dai ya ba galibin mazauna yankin Paso mamaki saboda yadda aka gama sallah da Rayyanu lafiya kalau

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Wani mutum ɗan kimanin shekaru 32 da aka bayyana sunansa a matsayin Rayyanu, ya rasu a masallaci bayan kammala sallar asubah a birnin tarayya.

Lamarin wanda ya ba galibin mazauna yankin mamaki da al'ajabi, ya faru ne a Unguwar Paso da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada a Abuja.

Abuja.
Wani Mutumi ya rasu a masallaci bayan sallar asubah a Abuja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

A rahoton da Daily Trust ta tattaro, wani mazaunin yankin, Ibrahim Musa, ya bayyana cewa ana tunanin mutumin ya rasu ne da misalin ƙarfe 5:56 na safe ranar Talata.

Kara karanta wannan

Dambarwar masarauta: Gwamnatin Abba ta aika sako ga 'makiya Kano'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda mutumin ya rasu a masallaci

A cewarsa, Rayyanu ya zo masallaci domin gudanar da sallar Asuba tare da sauran al’ummar musulmi da safiyar Talata, amma sai gawarsa aka fito da ita.

Da yake ba da labarin yadda lamarin ya faru, Ibrahim ya ce bayan kammala sallah, Rayyanu, wanda ya zo da babur, ya zauna domin ɗan hutawa.

Wasu sun ce ya kwanta kaɗan cikin masallacin saboda gajiya ko rashin isasshen barci, amma daga bisani ba a sake jin motsinsa ba.

A cewar Ibrahim Musa, da misalin ƙarfe 7:28 na safe, wasu masu tsaftace masallacin sun iso domin share wurin, sai suka lura da shi kwance ko motsi ba ya yi.

Sun yi ƙoƙarin su tashe shi domin ya ba su wuri su yi shara tare da tsaftace masallacin amma bai nuna wani alamun rai ba.

Bayan sun lura cewa ba ya amsawa, sai suka suka kira wasu dattawan unguwar domin su zo su ga abin al'ajabin ya faru.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗauki zafi da aka nemi Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Benuwai

An yi ƙoƙarin kai shi asibiti

Nan take suka garzaya da shi zuwa asibiti domin a ba shi kulawa amma likitan da ke bakin aiki ya duba shi, ya tabbatar da cewa Rayyanu ya rasu.

Daga baya, an sanar da danginsa, kuma an miƙa gawarsa ga iyalansa domin a yi masa jana’iza bisa koyarwar addinin Musulunci.

Duk da girman lamarin, babu wani rahoto da aka kai wa rundunar ‘yan sanda dangane da mutuwar Rayyanu.

Birnin tarayya.
Allah ya yi wa wani bawan Allah rasuwa bayan sallar asubah a masallaci a Abuja Hoto: Getty Image
Asali: Facebook

Sai dai mazauna yankin sun bayyana alhini da jimami, tare da yin addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta masa kura-kuransa.

Wasu daga cikin mutanen yankin sun ce yana da kyau a rika yin gwaje-gwajen lafiya akai-akai domin kaucewa irin wannan lamari, musamman ga matasa da ke fama da gajiya ko matsalolin rashin lafiya da ba su sani ba.

Wata mata ta rasu a wurin tafsir a Abuja

A wani labarin, kun ji cewa wata da ake kira Maman Zainab ta rasu a wurin tafsirin Alƙur'ani mai girma a masallacin Gawu da ke Abuja.

An ruwaito cewa matar ta fito daga gida lafiya tare da wasu makwabta uku domin halartar tafsir da ake yi a lokacin azumin Ramadan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng