Katsina: 'Yan Sanda Sun Dakile Mugun Nufin 'Yan Bindiga, Sun Kubutar da Bayin Allah

Katsina: 'Yan Sanda Sun Dakile Mugun Nufin 'Yan Bindiga, Sun Kubutar da Bayin Allah

  • Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun samu nasara kan miyagun ƴan bindiga masu tayar da zaune tsaye
  • Ƴan sandan sun daƙile wani yunƙuri da ƴan bindigan suka yi na yin garkuwa da mutane a titin Dandume-Funtua a ranar Litinin
  • Jami'an tsaron sun ceto mutanen da aka yi ƙoƙarin sacewa bayan sun yi artabu mai tsanani da ƴan bindigan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta samu nasarar daƙile harin ƴan bindiga.

Jami'an ƴan sandan sun daƙile yunƙurin da ƴan bindigan suka yi na sace mutane a kan titin Dandume-Funtua a ƙaramar hukumar Funtua

'Yan sanda sun kori 'yan bindiga a Katsina
'Yan sanda sun fatattaki 'yan bindiga a Katsina Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an ƴan sandan sun kuma yi nasarar ceto mutum bakwai ba tare da sun samu wasu raunuka ba.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun gwabza da 'yan bindiga, sun ceto mutanen da aka sace

Yadda ƴan sanda suka fatattaki ƴan bindiga

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 24 ga watan Maris da misalin ƙarfe 8:30 na dare.

Ƴan bindigan sun yi ƙoƙarin tsaida wata babbar mota da ke ɗauke da buhunan hatsi daga kasuwar Jabiri Funtua a kwanar Niyasu da ke ƙauyen Nasarawa.

Sai dai, direban motar ya ki tsayawa, lamarin da ya sa ƴan bindigan suka buɗe wuta, wanda hakan ya sa motar ta ƙwacewa direban, sannan ta faɗa wani rami.

Bayan samun rahoton lamarin, DPO na ƴan sandan yankin Dandume ya gaggauta tura jami’an tsaro na Operation Sharan Daji, waɗanda suka fafata da ƴan bindigan.

Bayanai sun nuna cewa ƴan bindigan sun tsere zuwa cikin daji ɗauke da raunukan harbin bindiga, inda suka watsar da shirin su na yin garkuwa da mutanen da ke cikin motar.

Dukkanin mutane bakwai da ke cikin motar sun tsira ba tare da wani rauni ba, kuma an mayar da su ga iyalansu cikin ƙoshin lafiya.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, an samu asarar rayuka

Jami'an tsaro na kare rayukan mutane

Wannan nasara ta ƙara nuna irin ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi a jihar Katsina don ganin an daƙile ayyukan miyagun ƴan bindiga.

Rundunar ƴan sanda ta yi kira ga al’ummar yankin da su ci gaba da bayar da haɗin kai da kuma samar da bayanan sirri don hana aikata miyagun laifuffuka.

Jihar Katsina dai na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar hare-haren ƴan bindiga, musamman a yankunan karkara, inda jama’a ke yawan fuskantar hare-hare, fashi da garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.

Ƴan bindiga sun farmaki jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu asarar rayuka bayan ƴan bindiga sun yi wa ƴan sa-kai kwanton ɓauna a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun hallaka aƙalla jami'an tsaro guda tara bayan sun farmake su a ƙaramar hukumar Anka ta jihar.

Jami'an ƴan sa-kan dai na kan hanyarsu ta komawa gida ne bayan sun ragargaji wasu ƴan bindiga lokacin da aka yi musu kwanton ɓaunan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng