An Shiga Fargaba, 'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Farmaki Sansanonin Sojoji a Borno
- Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai hare-hare a wasu sansanonin sojoji da ke jihar Borno lokacin da ake sa ran cin karfinsu
- Miyagun sun kai hare-haren ne a sansanonin sojojin da ke ƙananan hukumomin Damboa da Gambaru Ngala a ranar Litinin
- Sanata Ali Ndume wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya koka kan yawaitar hare-haren Boko Haram a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Wasu ƴan ta’adda da ake zargin na Boko Haram ne sun kai hari a sansanin sojoji na Wajirko da ke yankin ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno.
Ƴan ta'addan sun kuma kai wani harin a sansanin sojoji da ke ƙauyen Wulgo na ƙaramar hukumar Gamboru Ngala ta jihar Borno.

Asali: Original
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa aƙalla sojoji biyu sun rasa rayukansu bayan motarsu ta taka wani bam.

Kara karanta wannan
Rundunar sojojin saman Najeriya ta saki bama bamai a Borno, an hallaka 'yan ta'adda
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan Boko Haram sun farmaki sojoji
Motar sojojin wacce ke raka sabon kwamandan rundunar Operation Hadin Kai da aka tura Damboa ta taka nakiyar da ƴan ta’addan suka binne ne a kan titin Maiduguri-Damboa-Biu.
Rahotanni sun nuna cewa sabon kwamandan rundunar (wanda ba a bayyana sunansa ba) yana daga cikin waɗanda suka jikkata a harin.
Wannan lamarin ya faru ne a daidai lokacin da gwamnati da hukumomin tsaro ke shirin sake buɗe hanyar Maiduguri-Damboa-Biu mai tsawon kilomita 185, wadda aka rufe shekaru da dama saboda rashin tsaro.
Ƴan ta’addan sun kitsa kwanton ɓaunan ne a lokaci guda kan sansanonin sojojin Wajirko da Wulgo a ranar Litinin, wanda hakan ya sa dakarun sojoji suka janye daga wuraren.
Sai dai wani rahoto da har yanzu ba a tabbatar da shi ba ya nuna cewa an kashe wasu daga cikin ƴan ta’addan a harin.
Sanata Ndume ya koka kan harin Boko Haram
A halin da ake ciki, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya bayyana damuwa kan sake yawaitar hare-haren Boko Haram, musamman a yankunan kudancin jihar Borno.

Asali: Twitter
Yayin wata hira da manema labarai a Maiduguri a ranar Talata, ya ce abin takaici ne yadda hare-haren ke ƙara yawaita ba tare da daƙile su yadda ya kamata ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ya ce duk da cewa sojoji da sauran hukumomin tsaro na ƙoƙari, dole ne gwamnatin tarayya ta farka daga barci domin magance tushen matsalar ta hanyar amfani da fasahar zamani kamar jiragen yaƙi marasa matuƙi, don kawo ƙarshen ƴan ta'addan.
Sanata Ndume ya yi kira ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta inganta ba da horo, kayan aiki, makamai, da kuma jin daɗin dakarun Najeriya da sauran hukumomin tsaro.
Haka nan, Sanatan ya nuna damuwa kan yawaitar sace mutane a kan hanyar Maiduguri-Damaturu-Buni Yadi-Biu.
Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare masu zafi kan ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda masu tare da lalata motocin yaƙi guda uku na miyagun a hare-haren da suka kai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng