Lauyan Natasha Ya Cire Tsoro, Ya Fadi Masu Son Ganin An Kwace Kujerarta a Majalisa

Lauyan Natasha Ya Cire Tsoro, Ya Fadi Masu Son Ganin An Kwace Kujerarta a Majalisa

  • Lauyan da ke kare Natasha Akpoti-Uduaghan ya yi magana kan yunƙurin da ake yi na raba ta da kujerarta a majalisar dattawa
  • Barista Victor Giwa ya zargi gwamnatin jihar Kogi da ɗaukar nauyin yunƙurin da ake yi na yi wa Sanata Natasha kiranye
  • Lauyan ya nuna cewa akwai siyasa cikin shirin ganin an raba Natasha da kujerarta saboda ta na jam'iyyar adawa ta PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Victor Giwa, ɗaya daga cikin lauyoyin da ke kare Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ya yi sabon zargi kan yunƙurin yi wa sanatar kiranye.

Lauyan ya zargi gwamnatin jihar Kogi da ɗaukar nauyin ƙoƙarin raba Sanata Natasha mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya da kujerarta a majalisar dattawa.

Lauyan Sanata ya zargi gwamnatin Kogi
Lauyan Natasha ya zargi gwamnatin Kogi da daukar nauyin yi mata kiranye Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

Victor Giwa ya bayyana hakan ne yayin da ake tattaunawa a shirin Sunrise Daily na tashar Channels tv a ranar Talata.

Kara karanta wannan

"Ta kai ƙorafi LPDC," Natasha ta sake kinkimo rigima, ta zargi Sanata da 'rashin ɗa'a'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan Natasha ya zargi gwamnatin Kogi

Lauyan ya ce gwamnatin jihar, ta hannun ɗaya daga cikin hadiman Gwamna Usman Ododo mai suna Charity Omole, na jagorantar yunƙurin tsige Natasha Akpoti-Uduaghan daga kujerarta.

A ranar Litinin, 24 ga watan Maris, 2025, Omole, hadimar Gwamna Ododo, ta jagoranci wasu mazauna Kogi ta Tsakiya don miƙa koke ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), domin neman yi wa Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye.

Giwa ya ce yunƙurin yi wa sanatar kiranye, yana da nasaba da siyasa, kuma gwamnatin jam’iyyar APC a jihar ce ke ƙoƙarin ganin an cire ta saboda ƴar PDP ce.

Lauyan ya soki dalilan da aka bayar kan yunƙurin yi wa Natasha kiranye, ya na mai cewa ba su shafi ayyukanta ko cancantarta ba, illa saboda ta zargi Akpabio da cin zarafi.

Gwamna Usman Ododo
Gwamna Usman Ododo na Kogi Hoto: Alhaji Usman Ododo
Asali: Facebook

Giwa ya kuma zargi gwamnatin jihar da ɗaukar nauyin wannan yunkuri ta hannun Omole.

Kara karanta wannan

Sanatan Bauchi ya ba mutane kunya da azumi, bidiyosa yana rabon kuɗi ya shiga intanet

“Gaskiyar magana ita ce, ba yadda za a yi wannan shirin ya yi nasara sai dai idan an yi amfani da maguɗi."
“A wannan yanayin, macen da ta jagoranci wannan yunƙuri ita ce babbar hadimar gwamnan Kogi kan harkokin mata da matasa. Idan ka duba za ka ga wannan shiri ne da gwamnati ke ɗaukar nauyinsa, ba mazauna yankin ba."
“Charity Ijese Omole, a halin yanzu, ita ce babbar hadimar gwamnan Kogi kan harkokin mata da matasa. Don haka wannan yunƙuri da alama ba daga mutanen yankin ya fito ba, sai dai daga gwamnati."
“A tsarin yi wa sanata kiranye, dole ne mazauna yankin su fara yunƙurin, amma a wannan lamari, ana iya ganin yadda gwamna ke ƙoƙarin aiwatar da abin da yake son ya yi."

- Victor Giwa

Har zuwa lokacin da aka kawo wannan rahoto, gwamnatin jihar Kogi ba ta mayar da martani kan waɗannan zarge-zarge ba.

Natasha ta musanta ba majalisa haƙuri

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Jerin gwamnonin da suka goyi bayan Tinubu a dakatar da Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Natasha Akpoti-Uduaghan ta musanta rahotannin da ke cewa ta nemi afuwar majalisar dattawa kan dakatarwar da aka yi mata.

Sanata Natasha ta bayyana cewa har yanzu tana nan kan bakanta, kuma babu wanda ta nemi afuwarsa kan dakatar da ita da aka yi na watanni shida.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel