Rundunar Sojojin Saman Najeriya Ta Saki Bama Bamai a Borno, An Hallaka 'Yan Ta'adda

Rundunar Sojojin Saman Najeriya Ta Saki Bama Bamai a Borno, An Hallaka 'Yan Ta'adda

  • Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta kai farmakin sama a wani sansanin ‘yan ta’adda a Arewacin Chiralia, yankin Timbuktu Triangle
  • Kakakin NAF, Captain Kabiru Ali, ya ce farmakin ya biyo bayan sahihan bayanai na ganin motocin ‘yan ta’adda su na zirga-zirga a yankin
  • An harba rokoki da harsasai, wanda ya ragargaza motocin biyu nan take, sannan wani karin hari ya lalata motar yaki ta uku gaba ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta ce hare-haren da jiragenta suka kai sun lalata motocin yaki guda uku tare da hallaka 'yan ta’adda da dama.

An ce sojoji sun kai hare-haren ne a wani sansanin ‘yan ta’adda da ke Arewacin Chiralia, a yankin Timbuktu Triangle, wanda aka dade ana fama da matsalar tsaro a cikinsa.

Kara karanta wannan

Ana jimamin mutuwar mahaifiyar gwamna, kakakin ƴan sanda ya rasu

Rundunar sojin sama ta yi magana da ta kakkabe 'yan ta'adda a jihar Borno
Rundunar sojojin saman Najeriya ta yi wa 'yan ta'adda ruwan bama-bamai a Borno. Hoto: @NigAirForce
Asali: Twitter

Sojoji sun saki bama-bamai kan 'yan ta'adda

Mataimakin kakakin NAF, Group Captain Kabiru Ali, ya bayyana cewa an kai farmakin ne bayan samun sahihan bayanai daga sojojin kasa, inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanan sun nuna cewa ‘yan ta’addan suna zirga-zirga daga Sabon Gari zuwa Chiralia da motocin yaki guda uku, lamarin da ya haddasa kai farmakin.

Ali ya ce rundunar sojin saman Najeriya ta hanzarta aika jiragen yaki domin aiwatar da harin sama na 'AI' a yankin.

Bayan isowarsu wurin, matukan jiragen yaki na NAF sun hango ‘yan ta’adda da dama da kuma motocin yaki guda uku a ƙarƙashin bishiyoyi.

Yadda aka tarwatsa motocin 'yan ta'adda 3

An ce jiragen yakin sun kai hare-hare ta hanyar sakin bama bamai da harbin bindiga, inda nan take aka lalata motocin yaki biyu tare da kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan.

Yayin da ‘yan ta’addan ke kokarin janye motar yaki ta uku, wani gagarumin farmaki ya biyo baya, wanda ya lalata motar gaba daya.

Kara karanta wannan

Duniyar fina finan Najeriya ta yi rashi, fitacciyar jaruma ta rasu bayan mata tiyata

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), ya rahoto kakakin sojojin yana cewa:

"Cikin kwarewa da sanin abin harinsu, jiragen sojojin sama sun kai farmaki kan 'yan ta'adda, inda suka yi masu barin rokoki da na harsashi, wanda ya kai ga ragargaza motocin yaki biyu.
"A yayin da ‘yan ta’adda suka yi kokarin matsar da motar yaki ta uku, jirgin sojan ya sake kai wani karin farmaki, wanda ya lalata motar gaba ɗaya.
"Ƙarfin harin da aka kai ya ƙone dukkanin motocin, yayin da 'yan ta'adda masu yawa da suka yi yunkurin tserewa suka sheka barzahu."

Sojojin sama sun matsa lamba kan 'yan ta'adda

Sojojin sama sun durarwa 'yan ta'adda a Borno, sun yi masu ruwan bama-bamai
Borno: An kawo karshen 'yan ta'adda yayin da aka tarwatsa motocin yakinsu a wani harin sojin sama. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Hare-haren sun haddasa tashin wuta a wajen, bayan bama bamai sun dura kan motocin, sannan aka kara hallaka wasu ‘yan ta’adda da suka yi kokarin tserewa.

Sanarwar ta bayyana cewa wannan farmakin ya nuna aniyar rundunar sojin sama wajen murkushe ‘yan ta’adda da hana su damar yawo ko kuma shirya hare-hare.

Kara karanta wannan

Rivers: Abin da shugaban rikon kwarya ya yi ga ma'aikata bayan shiga ofis

Rundunar sojojin ta jaddada cewa za ta ci gaba da kai hare-hare don tabbatar da cewa ‘yan ta’adda ba su da mafaka a yankin Arewa maso Gabas.

Hedikwatar tsaro ta kasa ta tabbatar da goyon bayanta ga sojoji, a kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’ummar yankin baki daya.

Katsina: Sojojin sama sun ragargaji 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojojin saman Najeriya sun kai farmaki kan mafakar ‘yan bindiga a Faskari, Katsina, suka kashe 19, ciki har da shugabanninsu biyu.

Farmakin ya yi sanadiyyar rushe wasu manyan sansanoni biyu na shugabannin ƴan bindiga da aka daɗe ana nema kamar Gero (Alhaji) da Alhaji Riga.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng