Bauchi: Kakar Matasa Ta Yanke Saƙa, Za a Ɗauki Mutum 10,000 Aiki Ta Hanya Mai Sauƙi

Bauchi: Kakar Matasa Ta Yanke Saƙa, Za a Ɗauki Mutum 10,000 Aiki Ta Hanya Mai Sauƙi

  • Gwamnatin Bauchi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed za ta ɗauki matasa 10,000 aiki domin cike gurabe a ma'aikatu
  • Shugaban ma'aikatan jihar (HoS), Barista Mohammed Sani Umar ne ya bayyana hakan da ya kai ziyara hukumar ma'aikata ta Bauchi
  • Sani Umar ya ce gwamnatin za ta bude shafin yanar gizo na ɗaukar aiki wanda zai ba matasa damar shiga su cike bayanansu cikin sauƙi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye-shirye domin daukar matasa 10,000 aiki a ma'aikatu daban-daban na jihar.

Shugaban Ma’aikatan Jihar Bauchi (HoS), Barista Mohammed Sani Umar, ne ya sanar da haka yayin wata ziyara da ya kai ga Hukumar Kula da Harkokin Ma'aikata.

Gwamna Bala Mohammed.
Gwamnatin Bauchi za ta ɗauki matasa 10,000 aiki domin cike gurabe a ma'aikatu Hoto: Sen. Bala Mohammed
Asali: Twitter

Barista Mohammed ya ce wannan shiri na ɗaukar matasa aiki zai taimaka waje cike guraben aiki a ma’aikatun gwamnati da sassan da ke bukatar karin ma’aikata, Tribune Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sanatan Bauchi ya ba mutane kunya da azumi, bidiyosa yana rabon kuɗi ya shiga intanet

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilan ɗaukar matasa 10,000 aiki

Ya kara da cewa shirin zai kuma rage matsalar rashin aikin yi da zaman kashe wando da ya addabi matasa, sannan kuma zai ƙara inganta ayyukan gwamnatin Bauchi.

Shugaban ma'aikatan ya ƙara da cewa wannan shiri na daukar aiki na zuwa ne a daidai lokacin da sabon Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Ma'aikata ke fara aiki.

Bauchi za ta buɗe shafin ɗaukar aiki

A cewar Mohammed Sani Umar, gwamnatin jihar za ta buɗe shafin daukar aiki ta yanar gizo da matasa za su iya amfani da shi domin cike takardar neman aiki cikin sauƙi.

Shugaban ma’aikatan ya kuma tabbatar da cewa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya riga ya amince da daukar ma’aikata 10,000 a fannoni daban-daban na gwamnati.

Ya bayyana cewa za a yi kyakkyawan shiri na wayar da kai domin sanar da matasa yadda za su cike takardar neman aiki a shafin yanar gizon gwamnati.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya saba da tsarin jari hujja," NNPP ta haramta dokar ta ɓacin Ribas

Sannan ya yabawa Hukumar Fasaha da Sadarwa ta Jihar Bauchi (ICT) bisa yadda take gudanar da aikinta cikin kwarewa da kuma jajircewa, rahoton Leadership.

Gwamna Bala Mohammed.
Gwamnatin Bauchi ta waiwayi matasa domin rage zaman kashe wando a jihar Hoto: Sen. Bala Mohammed
Asali: Twitter

Ɗaukar matasa aiki babban ci gaba ne

A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Kula da Ma'aikatan Bauchi, Dr Ibrahim Alhaji Muhammad, ya bayyana wannan shiri a matsayin ci gaba babba ga matasan jihar da ke neman aiki.

Ya kuma jinjinawa gwamnatin jihar bisa kokarinta na amfani da fasahar zamani wajen samar da ingantaccen tsarin daukar ma’aikata, wanda zai hana magudi da tabbatar da adalci ga kowa.

Wannan shiri na daukar matasa 10,000 aiki a Bauchi babban ci gaba ne da zai taimaka wajen rage matsalar rashin aikin yi da kuma bunkasa ayyukan gwamnati.

Ɗan gwamna ya aika sako ga Seyi Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa ɗan gwamnan Bauchi, Shamsuddeen Bala Mohammed, ya buƙaci Seyi Tinubu ya ba matasan jihar aikin yi a ziyararsa maimakon raba abinci

Ɗan gwamnan ya jero irin tallafin da ya kamata Seyi ya riƙa ba matasa wanda suka haɗa da Keke Nafef, aikin yi ga waɗanda suka yi karatu da buɗe masu cibiyoyin fasaha.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng