Yadda Akpabio Ya Jawo Alkali Ya Cire Hannu a Shari'arsa da Natasha a Kotu
- Alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Mai shari'a Obiora Egwuatu, ya janye daga sauraron karar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
- Obiora Egwuatu ya dauki matakin ne bayan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya rubuta takardar korafi kan adalcinsa
- Tun da farko dai, kotun tarayya ta hana Majalisar Dattawa daukar matakin ladabtarwa kan Natasha, amma daga baya an janye umarnin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mai shari’a Obiora Egwuatu na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya sanar da janyewarsa daga sauraron karar da aka shigar kan dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Alkalin ya dauki wannan matakin ne a zaman kotu na ranar Talata, bayan da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya shigar da koke yana kalubalantar adalcinsa.

Kara karanta wannan
2027: Ta fara tsami tsakanin ƴan adawa, burin Atiku da maganar yanki na son ta da kura

Asali: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa alkalin zai mika takardun shari'ar domin a nada wanda zai cigaba da sauraron karar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukuncin kotun tun farko ya hana majalisa ci gaba da binciken Sanata Natasha, amma daga baya alkalin ya soke wannan umarni bayan bukatar da aka shigar a gabansa.
Dalilin janyewar Alkali Egwuatu a kotu
A zaman kotu na ranar Talata, yayin da alkalin kotun ke shirin ci gaba da sauraron karar, sai ya sanar da janyewarsa daga shari’ar.
Obiora Egwuatu ya ce ya dauki matakin ne saboda korafin da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya shigar kan cewa alkalin ba zai yi adalci a shari’ar ba.
Leadership ta wallafa cewa mai shari’a Egwuatu ya ce zai mayar da takardun karar zuwa ga babban alkalin kotun tarayya domin a ba wani alkalin da zai ci gaba da sauraron karar.
Abubuwan da suka faru a kotu a baya
A ranar 4 ga watan Maris, Mai shari’a Egwuatu ya bayar da umarnin wucin gadi da ke hana kwamitin ladabtarwa na Majalisar Dattawa ci gaba da binciken Sanata Natasha.
A cikin hukuncin, kotun tarayya ta ce ya zama dole a dakatar da binciken har sai an kammala shari’ar da ke gabanta.

Asali: Facebook
Yadda aka dawo binciken Natasha a majalisa
Duk da umarnin kotun, kwamitin ladabtarwa na Majalisar Dattawa ya ci gaba da zaman bincike kan Sanata Natasha kuma daga karshe aka dakatar da ita na tsawon watanni shida.
Bayan an shigar da wata bukata, Egwuatu ya sauya umarninsa, inda ya cire sashe na hukuncinsa da ya hana Majalisar Dattawa daukar mataki kan Sanatar.
A yanzu haka dai kallo ya koma kan kotun tarayya domin ganin matakin da za ta dauka saboda cigaba da shari'ar bayan alkalin ya zare hannunsa.
Akpabio ya sumbaci matarsa a idon duniya
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Goodswill Akpabio ya sumbaci matarsa a idon duniya yayin wani taro da aka shirya a jami'ar Calabar.
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya a kafafen sada zumunta, musamman a daidai lokacin da ake zarginsa da neman lalata da Sanata Natasha Akpoti.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng