'Za Ku Iya Halaka nan Take': Fitaccen Sarki Ya Gargadi Masu Neman Tuge Shi a Sarauta

'Za Ku Iya Halaka nan Take': Fitaccen Sarki Ya Gargadi Masu Neman Tuge Shi a Sarauta

  • Sarki Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya ce babu wanda zai iya cire shi daga sarauta, duk da kokarin da ake yi domin hakan
  • Basaraken ya ce labarin da ke cewa ya sha kaye a takarar sakataren sarakunan Yarbawa ba gaskiya ba ne
  • Ya bayyana cewa an kirkiri labarin ne domin a bata masa suna, amma ya ce ba ya shirin hada kai da masu son bata sunan wasu
  • Sarkin ya kara da cewa an sha kokarin cire shi daga mulki, amma duka sun fadi, kuma duk wanda ya sake yunkuri zai kara faduwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Fitaccen basarake, Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi ya yi magana kan makarkashiya da ake yi masa.

Sarkin na Iwo ya sha alwashi kan masu kulle-kulle inda ya ce babu wanda zai iya cire shi daga sarauta.

Kara karanta wannan

Barau: An saki adadi da bayanin tantance matasan da suka nemi tallafin Barau N5m

Basarake ya gargadi masu neman tuge daga sarauta
Sarkin Iwo, Abdulrosheed Adewale Akanbi ya ja kunnen masu kitsa masa makarkashiya. Hoto: Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi .
Asali: Facebook

Basarake ya kambama rawaninsa

A cikin wata sanarwa, Sarkin ya karyata labarin da ake cewa ya sha kaye a takarar zama sakataren kungiyar sarakunan Yarbawa, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Basaraken ya ce wannan kungiyar da ake magana kwata-kwata bai san da ita ba bare a ce yana neman matsayi.

Ya ce kuma rawanin Iwo na da daraja fiye da shiga irin wannan takara da ba ta da kima a cikin al'umma.

Sarkin ya ce labarin an kirkire shi ne domin a bata masa suna 'kuma a karkatar da hankalin mutane daga gaskiyar da ya fada kwanan nan'.

Ya ce:

“Shekarar da ta gabata, na samu labarin an shirya kafa kungiyar sarakunan Kudancin Najeriya, an gayyace ni, amma na ki zuwa.
"Ina da ayyuka da yawa da suka fi mani muhimmanci fiye da aiki tare da mutane masu tunani daban-daban.
"Bugu da kari, ba na halartar tarukan sarakunan Osun, na zabi tafarkin gaskiya kuma ba zan sauya wannan hanya ta Allah ba.”

Kara karanta wannan

Basarake ya nemi taimako bayan barazanar kisa da wasu matasa ke yi masa

Sarki ya fadi yadda ake shirya masa munafurci yana tsallakewa
Sarkin Iwo, Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi ya sha alwashi kan masu yi masa makarkashiya. Hoto: Oba Abdulrosheed Akanbi.
Asali: Facebook

Sarki ya gargadi masu neman kwace sarautarsa

Basaraken ya kara da cewa irin ayyukan da yake yi ya sha bamban da na sauran mutane.

A cewarsa:

"Yadda muke gudanar da abubuwanmu ya sha banban, shi yasa ake kyamata ta kuma ake magana kaina, amma ku sani, ban damu ba.”

Ya jaddada cewa babu wanda zai iya cire shi daga sarauta, ya ce an sha gwada hakan sau da dama amma ba a samu nasara ba.

Sarkin ya bayyana cewa masu kokarin cire shi ba su da nasara, kuma za su ci gaba da samun faduwar arziƙi.

Ya ce ba ya son hada kai da masu son bata wa wasu suna, kuma gulma da sharri ba za su hana shi bin hanyar da ya zaba ba.

“A maimakon haka, wadannan matsaloli ne suke kara mani karfi, duk wanda ya fahimta yana iya tsira daga halaka."

- Cewar basaraken

Mulkin Tinubu: Sarkin Iwo ya shawarci ƴan Najeriya

Kara karanta wannan

Bayan jita jita, Fubara ya bayyana a bainar jama'a da ya kawo karshen rade radi

Kun ji cewa babban basaraken masarautar Iwo a jihar Osun, Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi ya shawarci ƴan Najeriya da su yi wa shugaba Tinubu uzuri.

Babban basaraken ya ce cire tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya yi, abu ne mai kyau wanda zai amfani ƴan Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng